Yadda Zaka Nemi Katin Dan Kasa Ta Wayarka

Yadda Zaka Nemi Katin Dan Kasa Ta Wayarka

Menene Katin Dan Kasa?
Shine kati/takardar shaidar cewa mutum dan Nigeria ne.

Matsayin Katin Dan Kasa:
Katin dan kasa wajibine akan duk wani dan Nigeria da ya kai shekara 16 zuwa sama a duniya.

Ana Zama Dan Nigeria Ta Hanyoyi Kamar Haka:
1. Wanda aka haifa a Nigeria ko da kuwa Iyayensa ba ‘yan Nigeria bane indai an haifeshi a Nigeria.
2. Wanda aka haifa daga ranar samun ‘yan cin kai.
3. Wanda aka haifa a wata kasar amman iyayensa ‘yan Nigeria ne, ko kuma daya daga cikin Iyayensa.
4. Dan kasar waje da ya auri ‘yar Nigeria, sai ya dawo Nigeria da zama, shima zai zama dan Nigeria.
5. Wanda shugaban kasa ya bashi shaidar cewa ya zama dan kasa (sai dai wannan ban sani ba ko za’a iya yi masa katin dan kasa).

Yadda Ake Yin Register Katin Dan Kasa:
Akwai hanyoyi guda biyu da ake register katin dan kasa sune kamar haka:

*Hanya Ta Farko*
Ka nema ta waya ko ta computer dinka.

*Kaje shafinsu wato https://www.nimc.gov.ng
*Sai ka shiga “Free Enrolled”
*Zasu baka dama ka shigar da bayananka da na mahaifinka d.s.
*Idan ka gama shigarwa zai budo maka shafi da zakayi printing dinsa, shafin yana dauke da Bar Code zaka ganshi baki mai kama da alamar Thumb print.

Abubuwan Da Kake Bukata Domin Fara Register:
1. Email Address dinka
2. Network mai kyau na browsing

*Bayan kayi printing takardar zakaje babbar center da ake yin katin zaben.
*Idan ka kai musu takardar zasu yi scanning dinta zata fito musu da bayananka da ka shigar a wayarka ko computer.
*Sai su baka dama kayi thumb  print.
*Daga nan zasu fitar maka da National Identification Number (NIN).

*Hanya Ta Biyu Da Ake Yin Katin Dan Kasa*
Zuwa Kafa Da Kafa.
*Za kaje office din hukumar mafi kusa da kai.
*Zakaje da daya daga cikin wadannan abubuwan:-
1. Takardar shaidar haihuwa.
2. International Passport
3. Katin Zabe
4. Driving license
5. Tsohon katin dan kasar ka.

*Sharadi*
Dole ya zama takardar da zaka kawo daga cikin wadancan ya zama kwanan watan dake jiki shi kake so a saka maka a katin dan kasar.

*Daga nan zaka zo ayi maka hoto da thumb print.
*Daga nan a baka National Identification Number (NIN).

Game Da Lambar NIN:
Wannan lambar da za’a baka lambace ta musamman da kowa tasa dabance babu wanda za’a baiwa wannan lambar bayan kai, kuma kada ka mutu wannan lambar takace.
Yanzu haka anyi doka ba zaka iya yin International Passport don fita daga Nigeria ba har sai kana da wannan lambar.

Yadda Zakayi Idan Ka Manta Lambar Nin Dinka:

Idan ka manta lambar NIN dinka to kawai ka danna *346# a layin da ka bude dashi.

Daga Nan Sai Me Ya Rage?
*Daga nan za’a baka katin dan kasa na wucin gadi Temporary National Identity Card, ya danganta da inda kaje wani wurin za’a ce kaje ka dawo saboda sai an tara, wani gun kuma nan take ake yi maka.

Matsayin Katin Dan Kasa Na Wucin Gadi:
Shima katin dan kasa ne zai yi maka aiki kamar yadda wancan zai yi maka.

Abubuwan Da Zaka Iya Yi Da Katin Sune:
1. Bude account a banki
2. Yin International Passport
3. Da sauran abubuwan da ake bukatar ka saka Valid ID Card.

Abinda Katin Wucin Gadi Ba Zai Yiba.
Ba zaka iya cirar kudi dashi a account dinka na banki ba sabanin dayan shi kamar ATM zaka iya amfani dashi ka ciri kudi.

Yadda Zaka Karbi Katin Dan Kasarka:
*Bayan wasu watanni ko shekaru zaka ga sanarwa cewa wadanda sukayi katin dan kasa daga wata/sekara kaza zuwa wata/shekara kaza ya fito sai kaje ka karba.
*Ko kuma ka dinga shiga shafinsu na internet ka shigar da lambarka ta NIN zai fada maka cewa katinka ya fito yana office kaza a garinku ko kuma a’a Katinka bai fito ba ka cigaba da jira.

Shin Ana Biyan Kudi Wajen Yin Katin Dan Kasa?
Kyautane yin katin dan kasa duk wanda ya karbi kudinka da sunan katin dan kasa kayi report dinsa ga jami’an tsaro.

Yaya Zakayi Idan Ka Batar Da Katin Dan Kasarka?:
Idan katin dan kasarka ya bata to zakaje ofishin hukumar kayi bayani za’a baka dama kayi thumb print ko kuma idan ka rike lambarka ta NIN a saka sai a sake fitar maka da wani.

Wuraren Da Ake Yin Register A Kano:
1. Tal’udu Dai-dai Kwanar F.C.E.
2. Farm Centre Layin Cool Wazobia, Arewa Radio, da kuma Liberty TV.
3. Hotoro Yana Kallon Depot na NNPC.
4. Asibitin Aminu Kano.
5. Da sauran kananun cibiyoyi kamar a karamar hukumar hukumar Birni KMC anayi a Ofishin Wakilin Kudu dake Unguwar Gini, Kofar Kudu, bayan sakatariyar karamar hukuma.

Allah Ya Taimaka.

Thabit Muhammad Ala

Email:[email protected]

Whatsapp:08182373285

26, December 2018.

Leave a Reply

Your email address will not be published.