AN SAKI YAN AGAJIN IZALA DA AKAYI GARKUWA DA SU.

Wannan  Labari  Ya  Faranta  Zuciyar  Duk  Wani  Me  IMANI  Da  Tausayi  Gamida  Soyayyar  Juna  Da  Take  Tsakaninmu !

Alhamdu LILLAHI ala Kulli Haal . . .

‘Yan Uwanmu ‘Yan Agajin Da Akayi Garkuwa Dasu ALLAH Ya Kubutar Dasu Daga Hannun Azzalumai Marasa Imani

Idan me karatu bai mance ba dai a sati biyun da suka gabata ne wasu marasa Imani sukayi garkuwa da wadannan bayin ALLAH ‘yan Agaji, kan hanyarsu ta komawa gida garin Issaa dake jahar SOKOTO

Bayan sun dawo daga taron karawa ‘yan Agaji sanin makaman aiki a garin Dutse babban birnin jahar JIGAWA 

Ya UBANGIJI Kasa hakan yazama sanadin nauyaya mizaninsu na Alkhairi

Ya ALLAH Kar Ka Kara Baiwa Irin Wadannan Azzaluman Dama Akan Koma Wanene A Doron Kasa

Alhamdu LILLAHI !

Alhamdu LILLAHI !!

Alhamdu LILLAHI !!!

Leave a Reply

Your email address will not be published.