MATA DA DAMA MAZAJEN SU SUKAN HANA SU AIKI…. !!!

MATA DA DAMA MAZAJEN SU SUKAN HANA SU AIKI…. !!!
.
Mata da dama Suna yawan korafe-korafe game da hanasu fita domin yin aikin gwamnati ko waninsa wanda mafi yawa suke daukan al’amarin a matsayin an tauye musu hakki Wanda hakan ya jawo mutuwar aure da dama acikin al’umma da kuma rashin kwanciyar hankali a gidajen ma’aurata hakan yasa nayi wannan Dan takaitaccen rubutun.
.
A zahirin gaskiya akwai dalilai da dama da zasu sanya a hana mace aiki musamman idan muka yi duba zuwa ga abubuwan dake wakana acikin wannan zamanin. Kuma wannan ba lallai bane ya zama tauye hakki ko mugunta ba, domin su mata halayyarsu ta banbanta haka nutsuwarsu, hankalinsu da tunaninsu dama tarbiyyarsu.
.
Akwai macen da kai da kanka ma zaka ce da ita taje tayi aiki ko kuma taje tayi karatu saboda nutsuwarta da sanin ya kamatanta da kokarin tsayuwa akan iyaka da sauransu, amma wata macen kai karan kanka kasan idan ka bata wannan damar to hakika abunda zata aikata kare ma bazai ci ba.
.
Idan muka koma ga gata da musulunci yayiwa mace tun daga Ayoyin ALLAH da hadisan Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) zamu ga cewa shi dai musulunci ya zabawa mace zaman gida shine mafi alkhairi agareta, wanda basai na kawo su ba, saboda kada rubutun yayi tsayi da yawa.
.
● Sheikh Uthaymeen (Rahimahullah) yake cewa: “Su mata harkokinsu yana kasancewa ne acikin gida, amma shi neman arziki (Dukiya) da jihadi da abunda keda alaka da lamuran zahiri (ababen da ake yinsu awaje) wannan ya shafi maza ne kadai.” [Sharhul iqtida’u 204]
.
A gefe guda kuma akwai masu ganin sun daidaita hakkokin mace da namiji a matsayin daidaito wadanda suke ganin duk abunda namiji zai iya to mace ma zata iya yinshi, rashin daidaita mace da namiji 50/50 shi suke gani a matsayin tauyewa mace hakkinta wannan sune ‘Yan boko Aqeedah Wanda hukunce-hukuncesu ya sabawa ka’idar addini.
.
●Sheikh Muhammad Al-amin Al-Shanqidi (Rahimahullah) Yace: “Ka Sani, ALLAH Yayi min gamon-katar ni da kai ga abunda yake so kuma yake yarda dashi, cewa wannan karkataccen ra’ayin, mai sabawa halitta da hankali, da wahayin da yazo daga sama da shari’ar mahalicci, Gwani cikin halitta wanda ke qira ga daidaita maza da mata acikin dukkan hukunce-hukunce, da kuma ako wani fage na rayuwa, acikin wannan ra’ayi akwai barna da lalata tsarin rayuwar al’ummar ‘yan adam da basa boyuwa ga wani inba wanda ALLAH Ya toshe basirarsa ba.
.
→ Dalili kuwa shine ALLAH mabuwayi mai daukaka acikin hikimarsa wajen halitta, ya halicci mace da wata halitta ta daban, da ya sanyata ta dace da bada gudumawa daban-daban wajen gina al’umma, babu Wanda zai dace da bada wannan gudumawar idan ba ita ba.
.
→ Wannan kuwa ya hada kamar daukan ciki, da haihuwa da shayarwa da tarbiyar yara da hidimar gida da kula da ayyukan gida kamar girki da shara da abunda yayi kama da wannan, wad’annan hidimomi da mace take yi ga al’umma acikin gidanta, cikin sutura da killata da kame-kai da kiyaye mutunci da kyawawan dabi’u, da al’adu nagari, basu gaza hidimar da namiji yake yi ba wajen fadi-tashin neman abinci.
.
→ Wadancan wawaye jahilai daga cikin kafirai da ‘yan korensu suna riyawa cewa mace tana da hakkin yin aiki awaje da gidanta kamar yadda namiji yake dashi, tare da cewa alokacin da take da ciki Ko take shayarwa ko take cikin jego ba zata iya gogayya da wani aiki mai wahala ba kamar yadda kowa ya sani bisa al’ada.
.
→ To idan ita da mijin nata duk suka fice daga gida, duk ayyukan gida kamar lura da yara da shayar da na goye daga cikinsu da had’a abinci da abunsha ga namiji idan ya dawo daga aiki, duk sai su tozarta. Da zai dauki wani mutum aiki don ya kula da abunda macen take kula dashi na ayyukan gida, to da shi wannan mutumin da ya zauna aikin gida an dan kwafar dashi irin dankwafarwar da ita matar ta fita don guje mata. Don haka ba wata natijar kirki da aka samu, sannan gashi kuma fitar mace da rashin killatarta zubar da mutunci ne da tozarta addini.” [Tafseer Adawa’ul Bayan 3/422]
.
BABU LAIFI GA MACE TAYI AIKI idan har zata kiyaye dokokin ALLAH.
.
● Sheikh Salih Alfauzan (Hafizahullah) yake cewa: Mu dai ba muna yaki da fitar mace daga gida domin ta yi aiki bane idan dai an kiyaye wasu ka’idodi kamar haka:
.
1• Ta zama mabukaciya ce ga wannan aiki, ko kuma al’ummar da take cikinta ta bukatu da wannan aiki nata, idan ya zamanto babu mazan da zasu iya yinsa.
.
2• Yin aikin nata ya zamanto bayan ta riga ta bada hakkin gidanta, wanda yake shine aikinta na ainihi.
.
3• Wannan aikin ya kasance acikin mata ne, kamar koyar da mata, ko ta zama likita ko mai jinya ga mata ba tare da cakuduwa da maza ba.
.
4• Hakanan ma babu laifi, kai dole ne ma mace ta koyi al’amuran addininta. Babu abunda zai hana ta neman sanin abunda take da bukatuwa gare shi na al’amuran addininta, kuma wannan neman sanin ya zamanto acikin ‘Yan uwanta mata ne.
.
5•Haka kuma babu laifi gareta ta halarci karatu a masallaci ko makamancinsa, amma ta zamanto ta suturce kanta, kuma ta ke6e daga maza, kamar yadda mata suka kasance suna yi a farkon musulunci wajen koyarwa da neman ilimi da halartar masallatai.” [Takhtisu bil mu’aminaat]
.
Da wannan nake kira ga ‘Yan uwana mata da ki sani cewa zamanki a dakin mijinki shine mafi alkhayri agare ki, idan mijinki ya hana ki yin Aiki to kiyi hakuri ki rungumi aurenki, idan kuma ya baki damar yin aiki to kiji tsoron ALLAH ki kiyaye dokokin ALLAH kuma kada ki tauye hakkokin auren ki.
.
#Repost.
#FaridahBintuSalis.
#Bintusunnah.

Leave a Reply

Your email address will not be published.