SHIN KA LURA DA HAKAN KUWA?

Shin ka lura?

Duniya taci gaba, an canja abubuwa, da dama, wasu ma abun kunya ne ayi amfani dasu, musamman ga masu hannu da shuni.

Amma har yanzu doki bai canju ba, kai abun alfahari ne ma aganka a saman doki, har yanzu sarakunan duk duniya suna amfani da doki an gagara samun madadin sa.

Kuma bana tsammanin za’a samu madadin sa Insha Allah.

Mai kudi da talaka sarki da yan siyasa, suna hawan doki.

A zamanin baya,
Doki shine tankan yaki, Wanda za’a kutsa dashi ko ina wajen yaki.

Doki shine babban abun hawa na alfarma da duk Wanda ya mallake shi yanaji tamkar jirgin sama ne ya mallaka.

Gaskiya doki yayi wallahi ina son doki.🏇🏇🏇

Muhammad Ismail Ali.

Leave a Reply

Your email address will not be published.