HUKUMAR MASALLACIN SULTAN BELLO DA DAKATAR DA WA’AZIN IZALAN APC A KARKASHIN ABDULLAHI BALA LAU

*HUKUMAR MASALLACIN SULTAN BELLO DA DAKATAR DA WA’AZIN IZALAN APC A KARKASHIN ABDULLAHI BALA LAU*
By Al-amin Mukthar
Hukumar gudanarwa ta masallacin Sultan Bello jiya ta sanar da dakatar da wa’azi daya shafi siyasa wanda Izalan bangaren Sheikh Abdullahi Bala Lau ta shirya yi. Hukumar dai ta sanar da wannan matsayin ne bayan taron data kira na gaggawa don matsalar da wa’azin zata iya haifarwa a masallacin. Za’a iya tuna wa dai jiya, Wednesday 23rd January, 2019 kungiyar bangaren Izala a karkasin Bala Lau kwatsam ta sanar da yin wa’azi a masallacin batare da neman izinin hukumar ba. Daga cikin abubuwan da ya kawo cecekuce har yasa matasa mazauna Unguwan Sarki da sauran Unguwan ni na kewaye suka dauki alwashin dakatar da taron shine programme of event da Izalan Bala Lau ta sake wanda ya tabbatar karara taron sun kira ne don jaddada matsayin su na yin aiki a APC duk da duk yan takaran neman kujeran shugaban kasa dana gwamnan jihar Kaduna wato Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar, da kuma Nasir El-Rufai da Ashiru Kudan na PDP duk musulmai ne. Daga cikin wanda suka gaiyata daya nuna matsayin su a siyasa karara duk da Shugaban kasa Buhari a baya ya bada shawara a shuwagabannin addini su daina shiga harkan siyasa sun hada da Governor Nasir El-Rufai, Uba Sani, yan majalisan jihar Kaduna na APC da chairmen na local governments. Babu member na PDP guda daya da suka gaiyata. Har Senator Shehu Sani na jam’iyar PRP basu gaiyata ba wanda ya sake tabbatar da manufar su.
Sannan rohutun ni sun gabata cewa kungiyar sun karbi miliyan dari N600m daga gwamnatin APC sannan Governor El-Rufai ya baiwa Bala Lau jeep SUV guda biyu wanda har hotunan motocin an nuna kuma har yau kungiyar bata karyata ba. Ana ganin wannan yunkuri ne na Izalan Bala Lau su nunawa gwamnatin APC lailai suna musu aiki da kuma yaudaran su suyarda cewa duk mabiyan kungiyar na tare dasu wanda a zahiri ba haka bane.
A dalilin wannan rudanine wanda zai iya jefa masallacin cikin wani sabon fitina yasa kwamitin masallacin ta kira taron gaggawa don su dauki matsayi. Hukumar masallacin dai ta tabbatar wa manema labarai bata da wani dan takara daya tunda duk wanda suka fito musulmai ne. Sun kuma ce masallacin ba dandaline na siyasa ba. Sun kuma aika copy takardan da suka sake a manema labarai da komishin yan sanda na jihar Kaduna da darekta SSS na jiha.
A baya ma shugaban Izalan bangaren Bala Lau na jihar Kaduna, Tukur Isa yaso ya haddasa wata fitina a masallacin Sultan Bello inda kai tsaye ya rubuta takarda wai ya dakatar da dukkan Committee Members na masallacin, hurumin da ko shugaban shi Bala Lau bashi dashi. Haka kuma bayan rasuwan Sheikh Babantune, Tukur Isa kai tsaye batare da sannin hukumar masallacin ba yace ya nada wani Malami daga Zaria yaci gaba da karantar da littafin Mukthasar wanda marigayi Babantune ke karan tarwa, hurumin da Tukur Isa bashi dashi wanda kuma kai tsaye aka taka mishi birki. Littafin Mukthasar dai marigayi Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi ya fara karantawa a masallacin daga nan Sheikh Babantune yaci gaba, yanzu kuma Sheikh Dr. Ahmad Gumi wanda ya hau kujeran mahaifin shi gun shugaban cin masallacin ya ci gaba da karatun littafin.
Wani matashin Izala ya jinjinawa hukumar Sultan Bello da “Sheikh Abubakar Gumi Sultan Bello Mosque Foundation” da wannan matsayi da duk suka dauka kuma yace a shirye kullun suke su kare darajan wannan Masallaci mai albarka da tarihi. Ya kuma shawarci su Bala Lau suje kauyuka yin wa’azi inda aka fi bukatan shi yace malaman Sunna kamar su Sheikh Algarkawy suna iyakan kokarin su gun karantar da al’umma a kullun cikin masallacen jihohi. Yace abunda kawai ake bukata yanzu shine su Bala Lau su dinga amfani da dukiyoyin da suke samu zuwa kauyuka don isar da sakon Allah amma duk jihohi basu bukantar wa’azin nuna izza, neman duniya ko amfani da mumbarin manzon Allah don bada raddi. Ya kuma shawarce su in har don Allah suke yi subi umurnin Allah gun hada kan Izala a karkashin shugabanci DAYA.

Leave a Reply

Your email address will not be published.