Angabatar da taro Bita ga Yan Social Media na Jihar Gombe karo na farko

Angabatar da taro Bita ga Yan Social Media na  Jihar Gombe karo na farko 
Daga Musa H Musa. 
A Yau Asabar Kungiyar Izala ta jihar Gombe ta gabatar da Bita ga Yan Social Media na jihar Gombe wadda Shugaban kungiyar ta jiha Alhaji Salisu Muhammad Gombe ya jagoranta. 
Dayake jawabi Shugaban kungiyar ta jiha Engr Salisu Muhammad Gombe ya yayi kira ga dukkanin masu amfani da yanar gizo da sanya tsoron Allah acikin ayyukansu, sukuma gudanar da wannan kafafen bisa tsarin shari’a domin zai kasance abun tambaya a gobe kiyama, Sannan a guji bayar da labarin da bai ingantaba har sai an tatantan ceshi. 
Dayake gabatar da Takarda Shugaban Kwamitin a matakin kasa Alhaji Ibrahim Baba Suleiman yayi kira ga matasa da auguji harkan jagaliyancin yan siyasa a kafar yanar gizo, tare da kaucewa miyagun yansiyasa. Domin cimma manufarsu. 
Pro. Rashid Abdulganiy ya bayyana kafar social media a matsayin sabon al’amarin da yakamata a yada manufar addinin musulunci a cikinsa wadda hakan shine zai kai mutum ga tudun natsira 
Muhammad Ahmad Bindawa yagabatar da takardarsa mai taken yadda yakamata musulmai ya mu’amalanci social media. 
Taron yasamu halartan Shugaban kungiyar Jibwis ta jihar Gombe Alhaji Salisu Muhammad Gombe, Commissioner na matasa Alhaji Faruk yarma, da wakilin babban hakimin cikin gari Alhaji Yaya Hammari,Shugaban kwamitin Social media na kasa Alhaji Ibrahim baba Suleiman Shugaban Kwamitin a matakin jiha Malam Musa H Musa da Malamai da Yan agaji  Mahalarta daga dukkanin Kananan hukumomi  guda shadaya.
Muna Addu’ar Allah yasanya Albarka Cikin Abun da aka tattauna yakuma bamu nasararsu

Leave a Reply

Your email address will not be published.