Kungiyar Izala ta Jihar Gombe ta gabatar da da taron Bita ga dukkanin yan takarar siyasa a Jihar Gombe,

Kungiyar Izala ta Jihar Gombe ta gabatar da da taron Bita ga dukkanin yan takarar siyasa a Jihar Gombe, 
Daga Musa H Musa. 
Shugaban kungiyar izala ta jihar Gombe Alhaji Salisu Muhammad Gombe shine ya jagoranci shirya taron wadda yagudana a dakin taro na  Jami’a mallakar jihar Gombe.
Shugaban Hukumar zabe (Inec) ta jihar Gombe Alhaji Ibrahim Umar, shine Shugaban zama inda maigirma Gwamna yakasance babban bako na Musamman wanda yasamu wakilcin Kwamishinan Ilimi mai Dr Isa Wade 
Dayake jawabi Wakilin gwamna Alhaji Isa wade ya bayyana wannan taro a matsayin Abu mafi bukata ga yantakara domin wayar musu dakai da daukan siyasa bada gababa 
Dayake jawabi  Shugaban kungiyar ta jiha Alhaji Salisu Muhammad Gombe ya bayyana Makasudin shirya wannan taro, Duba da yadda babban zabe yatunkaro hakkin mune mu gayawa dukkan yan takara abun da yawajaba akansu na shugabanci domin addinin musulunci yakalli shugabanci yakuma samar mashi da tsari domin Al’umma suyi rayuwa mai tsafta. 
Dr Rashid Abdulganiy yagabatar da takardarsa mai taken Yadda Yakamata Dan takara yakasance, inda Shima Dr Sa’idu Ahamad Dukawa yagabatar akan Shugabanci a Musulunci. 
Yantakara daban daban sun bayyana  jin dadinsu akan wannan taro domin shine yafi cancanta Kungiyoyin addini su dinka shiryawa hakan shine zai sanya asamu jagorori na gari acikin Al’umma. 
Taron yasamu halartan yan takaran Gwamnoni, Yan Majalisu tarayya dana jiha,  Sanatoci daga Jam’iyyu Daban daban. da Sauran Al’ummar daga sassan jihar Gombe.55

Leave a Reply

Your email address will not be published.