INEC Adhoc staff Training ATBU

INEC Adhoc staff Training ATBU 
SANARWA
Bayan samun korafi da mukayi daga mutane wadanda ke zama a nesa kuma suka nuna buqatuwar su naso suyi wannan aiki yasa mukayi wannan rubutu saboda fayyace abubuwa, 
1. Shugabanci na SUG sun samu sanarwa akan batun INEC ta ofishin Registrar ne na ATBU ba ta wurin INEC ba,  dukkan sakonni da suka shafi INEC an tura su ne kai tsaye zuwaga ofishin Registrar,  shi kuma ya sanarwa SUG kan su sanarea dalibai.
2. Shugabancin SUG an basu dama ne kawai su tunatar da dalibai akan training wanda za’a fara shi 29th January, 2019, sannan babu wani sunaye da aka fidda daga ATBU
3. Mun samu labarin cewa an fidda sunayen dalibai a Abubakar Tatari Ali Polytechnic, Bauchi da kuma ofishin INEC na Bauchi. Sunayen da aka fidda, an fidda daga cikin wadanda sukayi register online.
3. Sannan akwai dalibai da suka bada application nasu ga kananan hukumomi wasun su an fidda sunayensu,  bamusan cewa shin wadanda dalibai zasuyi training a kananan hukumomin su ne koko zasu zo ATBU ne suyi training ba.  Shawarin da muke badawa shine wadanda suke nesa suyi training a kananan hukomominsu, matukar an fidda sunayensu. 
4. Kamar yadda aka sanar gobe talata 29th,  January za’a fara training a ATBU, ana buqatar dalibai suzo da ID CARD sannan za’a taru a Yelwa Campus da karfe 8:00 na safe. 
5. Dalibai wadanda basu aike da bayanasu ga INEC ba, kuma suna son yin wannan aiki na INEC zasu iya zuwa wannan training saboda za’a amfani da attendance ne ba application da akayi online ba. 
A karshe muna bada hakuri ga matsaloli da aka samu. 
Sa hannun 
Magatakarda
Comr. Musa Ali Musa
Yadawa
Mai hulda da jama’a
Abdussrmad I yakubu
Da
Sheba Y Queen
Daga
Shugaba
Rt. Hon. Muhammad Nazeer Ahmad
CSB
Fassarawa
#Abu Abdirrahman Kaltungo

Leave a Reply

Your email address will not be published.