Wanene VIO, kuma menene ayyukan sa?

Wanene VIO kuma menene ayyukan sa? 
VIO shine Jami’i mai duba lafiyar ababen hawa, a turance kuma na nufin Vehicle Inspection Officer (VIO) .
Aikace aikacen VIO
1. Duba lafiyar ababen hawa
Shi kuka wannan duba lafiyat ababen hawan,  an kasa shi kashi uku (3) 
(a) Pre registration inspection wato duba lafiyar abin hawa kafin ma a mishi regista, kafin a bashi lamba a matsayin an yadda ayi amfani da shi akan hanya. 
(b) period inspection wato duba lafiyar abin hawa lokaci zuwa lokaci 
Motoci na haya ana duba lafiyarsu duk bayan wata shida (6), Idan an gamsu da lafiyarsu sai a basu certificate.
Motocin gida kuma ana duba lafiyarsu ne na tsawon shawa goma sha biyu (12) suma idan an gamsu da lafiyar su sai a basu certificate.
Duk wanda yake amfani da mota ta aikin gida ma’ana private, duk tsawon wata goma sha biyu (12) sai yazo VIO ya sake duba lafiyar abin hawan shi sannan ya mishi izini ya cigaba da amfani da wannan abin hawan. 
Haka kuma duk wanda yake aiki da motar haya wato public vehicle shima bayan wata (6) zaizo wajen VIO domin duba lafiyar abin hawansa sannan a bashi izinin ya cigaba da amfani dashi.  
2. Inspection 
Shi wannan idan abin hawa ya afka cikin hatsari yan sanda zasu gayyaci VIO bayan sun gama nasu aune-aunen VIO zaizo ya duba wannan abin hawan, zaiyi la’akari da abubuwa guda uku (3) 
(i)  Zai duba lafiyar abin hawan kafin afkuwar wannan hatsarin
(ii) zai duba lahanin da aka samu sanadiyyar afkuwar wannaj hatsarin 
(iii) Zai duba yanayin wannan hatsarin, menene ya kawo wannan hatsarin ko kuma menene ya taimaka wajen afkuwar wannan hatsarin 
Wannan shi ake kira duba lafiyar abin hawa.
KOYAR DA TUKI (DRIVING) 
Baiwa duk wanda yakeso ya bude makarantar tuki izinin cewar ya bude private driving schol. 
Bada izinin tuki wato drivers license, bayan driving test kenan bayan an gwada mutum. 
Wato dokar VIO ne na gwada mutum ko ya iya tuki don a bashi shaidar tuki wato driving license da kuma bashi izinin jan wannan abin hawan. 
Hanyoyin hukunta wadanda suka ki bin doka
Idan aka samu mota marar lafiya za’a kama ta a duba ta kuma a bada irin gyare-gyaren da ya kama ta driver yayi, wani lokaci ma akan ajiye driver a Office sai an gama wannan gyare-gyaren sannan a duba ta, idan an gamsu da wannan da wannan gyare-gyaren sai a sakar masa da abin hawan sa.
Haka kuma idan drivers license ne lokutansa suka kare wato shaidar tuki yayi expire zasu sabunta mishi, idan kuma laifin yakai ga zuwa kotu, to VIO tanada hurumi da zata rubuta takarda ta tura kotu, sai kotu ta yanke hukuncinta sannan ta dawowa wannan hukuma da sakamakon hukuncin da ta yanke. 
HUKUNCIN WADANDA SUKE TUKI BADA LASISI BA
Duk wanda aka samu yana tuki babu driving license to akwai abubuwanda doka ta tanada ayi masa,  za’a iya kaishi kotu, kotu ta hukunta shi akan yana tuki ba izinin tuki kuma bayan wannan za’a zo a jarraba shi idan an gamsu ya iya sannan yabi hanyar da ake bi domin mallakar wannan lasisin, sannan a kyale shi ya cigaba da jan abin hawan shi. 
LAIFUKAN DA AKA FI SAMU A KANO
1. Rashin kyawun ababen hawa
2. Sakacin masu ababen hawa, basa so su canza takardun su. 
3. Rashin tuki da driving license 
4. Yin tuki da driving license na bogi. 
RASHIN LASISI YA TSAYA NE KAWAI GA MASU TUKI? 
An fi bada karfi ga masu motoci, amma zuwa yanxu hatta masu a daidaita-sahu akwai tsarin da akayi a kansu, domin kowane directa na jaha an umurce shi da ya horar da wadannan masu ababen hawan. 
Bayan an bawa mutum hoto, akwai buqatar a jarraba shi, shin ya iya jan wannan abin hawan, sannan a bashi izinin jan wannan abin hawan wato driving license.
Wannan ba sabuwar doka bace ga masu a daidaita sahu, hatta masu babur suma akwai dokar tasu tukin,  lallai ne sai an baki izini sannan kaje ka fara tuki,  saboda haka ba sabuwar doka aka kawo ba. Kawai za’a kara jaddada ta ne. 
Kira ga masu ababen hawa
1. Lallai ne ka tabbatar ka iya jan wannan abin hawan
2. Ka tabbatarda cewa kaje VIO ya jarraba ka ya baka izinin jan wannan abin hawan. 
3. Duk lokacinda kake kan hanya ka tabbatar da cewa kana tuki a cikin nitsuwa, kayi kulawa da dokoki da qa’idodin hanya da kuma haqqin sauran wadanda ka samu bisa hanya.
#Abu Abdirrahman Kaltungo 
CEO Arewagist.com.ng
28 January, 2019

Leave a Reply

Your email address will not be published.