Yayin da Shugaban kungiyar Izala ta Jihar Gombe Alhaji Salisu Muhammad Gombe yake ganawa da yan’jaridu akan taron bita guda biyu da kungiyar a matakin jiha ta shirya.

Yayin da Shugaban kungiyar Izala ta Jihar Gombe Alhaji Salisu Muhammad Gombe yake ganawa da yan’jaridu akan taron bita guda biyu da kungiyar a matakin jiha ta shirya.
Shugaban ya sanar da yan’jaridu cewa kungiyar ta Kalli Al’ummar jihar Gombe, takuma ga dacewar bayar da gudnmaowa domin dauradda zaman lafiya dakuma daura al’umma Manyansu da kananan su akan turba nagari. 
Wannan yasanya ta shirya tarukan, nafarko tagabatar wa matasa masu ta’ammuli da yanar gizo domin sanardasu abun da yawajaba akansu na hakkin juna dakuma bayar da gudnmaowa domin kawo zaman lafiya, da kaucewa bangar siyasa a yanar gizo. 
Taro na biya yahada gamayyar yan takara daga kowanne jam’iyya a dukkanin matakai na siyasa domin janyo hankulansu da gabatar da takara bisa yadda shari’a ta tanadar, da kaucewa dukkanin abun da zai kawo tozarta a bokin takara ko cin mutuncin wani.
Shugaban yace manufarmu shine Al’umma susamu shugabanci na gari suma shuwagabannin suzama nagari, kuma Muna musake nauyin da Allah ya dauramana mu isar da sakonshi ga bayinsa 
Sannan shugaba yace kuma nan gaba akwai wasu Bita na mata da kuma yan’agaji wannan kungiyar a matakin jiha duka domin saita al’umarmu zamu gabatar dashi da izinin Allah .
Jibwis Gombe

Leave a Reply

Your email address will not be published.