[[Hikima Kashin Kwance]] Maraya dan aji Shida (6) Firamare dake sana’ar gyaran kwan Lantarki

[[Hikima Kashin Kwance]] Maraya dan aji Shida (6) Firamare dake sana’ar gyaran kwan Lantarki

Muhd Aliyu Dan unguwar Sharada a birnin Kano wanda a yanzu haka yake aji Shida (6) a makarantar Firamare inda yake sana’ar bi wuri-wuri lungu-lungu da sako-sako na birnin Kano yana cewa akwai mai gyaran kwai domin ya gyara masa a biyashi, da wannan yake daukar nauyin kansa da kuma tallafawa mahaifiyarsa.

A tattaunawarsa da Basheer Sharfadi ya bayyana yadda ya faro wannan sana’ar da kuma irin yadda ya yake hada makarantun Boko dana Addini da kuma sana’ar tasa ba tare da daya ya cutar da wani ba.

Ya kuma bayyana irin kalubalen da ya fuskanta, da kuma burin da yake dashi a rayuwarsa.

A karshe yayi kira da ‘yan uwansa yara kan su dage su kuma maida hankali a bisa tsari irin na dogaro da kai.

Hausawa sukace waka a bakin mai ita tafi dadi, Shiga link dake kasa domin saurarar cikakkiyar tattaunawa da wannan Dan Baiwa, sannan kayi sharing ga abokananka don muma aga fasahar ‘yan uwan mu Hausawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.