Sheikh Kabir Gombe a Jigawa Gobe Alhamis da Juma’a

BABBAN SAKATAREN IZALAR NIGERIYA SHEIKH (DR.) MUHAMMAD KABIRU HARUNA GOMBE ZAI KAWO ZIYAYAR KWANA BIYU A JAHAR JIGAWA.

A madadin Kungiyar Jama’atu Izalatil bidi’ah Wa’ikhamatis-sunnah (JIBWIS) Reshen Jahar Jigawa. Karkashin Jagoranci,
Malam Abubakar Jibrin Hadejia.

Suna farin gayyatar ‘yan uwa musulmi zuwa Gagarumin wa’azi da, Babban  Sakataren Kungiyar Izalah na kasa,
As-sheikh (Dr.) Muhammad Kabiru Haruna Gombe.
Zai gabatar kamar haka;

 Na  Farko:
RANA: Alhamis 24-Juma-ul-Awwal-1440 wanda ya dace da, 31-January-2019.

LOKACI: Karfe 8:00Na Dare.

GARI: Garun Gabas Dake Karamar Hukumar Malam-Madori.

WURI: Kofar Maigirma Hakimin Garun Gabas

Na Biyu:
RANAR  Juma’ah za’a bude Masallacin Juma’ah A Garin Dandi dake   Karamar Hukumar Kazaure.

LOKACI: Misalin Karfe 1:00Na Rana.

Da Daddare Sheikh (Dr.) Muhammad Kabiru Haruna Gombe tare da Malaman da Kungiya ta kasa ta turo zasu gabatar da,Wa’azi A Kofar Maimartaba Sarkin Kazaure.
LOKACI:Karfe 8:00Na Dare.

Allah yaba ikon halatta Amin.

SANARWA DAGA:
P.A Baffa Maina Hadejia.

JIBWIS JIGAWA
29/January/2019.

Leave a Reply

Your email address will not be published.