ADALIN SARKIN GOMBE

ADALIN SARKIN GOMBE 
Daga Mansur Aliyu Saeed 
Mai Martaba Sarkin Gombe  Alh (Dr) Abubakar Shehu Abubakar III ‘Da ne ga Marigayi Mai martaba Sarkin Gombe na 10 Alh Shehu Abubakar kuma shine na biyu cikin Yayan Mai Martaba. An Sarkin Gombe Abubakar Shehu a ranar 17 ga watan 12 na shekarar 1977.
A bangaren karatu kuwa Mai Martaba yayi karatun addini da na zamani, a karatun Boko ya taka har zuwa matakin Digiri, yayi karanci fanni kimmiyyar siyasa wato Political Science a turance a Jami’ar Maiduguri dake jihar Borno ya kuma kammala a shekarar 2005. 
A ranar  27 ga watan mayu  na 2014 muka tashi da mummunan rashi na Dottijin Sarki Mai Martaba Gombe (Allah Ya jikan Sarki, Ya gafartawa Sarki) Allah Ubangiji shine ke bayar da mulki ga wanda ya so a  lokacin da Ya so ko ana so ko ba’a so, Ya damka  amanar al’umar Masarautar Gombe a hannun Mai Martaba Sarki Alhaji (Dr) Abubakar Usman Shehu Jikan Buba Yero
Bayan kasancewar Mai Martaba a matsayin Sarkin Gombe na goma sha daya yachi gaba da ayyukan raya al-ummah da jin kai da adalchi da gina addinin Islam kamar yadda ya gada, wadannan ayyuka sunyi matukar kara masa farinjini da kima a idon talakawan sa, ya kuma kare martaba ta wannan babbar masarauta.
Mai Martaba Sarki ya shafe shekaru da basu wuce biyar ba akan karagar mulki, amma idan zamu auna ayyukan alheri da ciyar da kasa da al’umar ta gaba da yayi to ko a shekara dari yayi sai sannu ballantana a shekara biyar. 
A fanin gudanar da mulki Mai Martaba Sarki yabar kofa a bude ga dukkan al’ummah ta yadda kowa yake samun dama da yancin ganin sa don kawo shawara ko gyara ko wani koke. Sarki yayi hakan ne domin tabbatar da mulkin al’uma gabadaya ne, a gudu tare a tsira tare, kuma hakan koyi da Sunnar ma’aiki kamar yadda yake shawari da sahabban sa duk da kasancewar komai nasa wahayi. 
Mai martaba Sarki ya samarwa matasa masu dimbin yawa admission a jami’oi da wuraren karatu da dama a kasar sa ta Gombe.
A  chikin watan Aprilun 2017  mai martaba sarki ya dauki nauyin marayu dubu uku ya sasu a makaranta ya dinka musu uniform da komai kyauta domin jiyar da su dadin duniya da dadin ilmi da kuma share musu hawayen maraici.
Haka ranar Asabat 19 ga watan 12 shekarar 2015 Mai Martaba Sarki ya tallafawa yan gudun hijra wanda rikicin boko haram ya rutsa dasu, ya tallafa musu da abinchi da kayan sawa wassu suka bar wurin chikin kukan farin chiki bisa  irin tallafin da uban kasa ya musu
 Zaman banza da rashin aiki ko Sana’a  babban ciwo ne dake addabar matasan mu, duk  mai hankali yana kwana yana tashi da wannan matsala da tunanin mafita. Ma Martaba Sarki yana iya bakin kokarin sa wajen samawa matasa ayyukan yi da sana’oi don kawar da zaman banza a tsakanin matasa ina iya tunawa a August 2017 Matasa da sarki yasama ma aikin sojan sama suka ziyarce shi   sanan a October shekarar wassu gun-gun matasan da aka samawa aikin dan sanda suka kai ziyarar bangirma da godiya ga mai martaba sarki 
Lallai alherin Sarki bai tsaya a nan ba da mutanen unguwar bolari suka kawo kukan a roki gwamnati ta Gina asbiti a bolari Sarki bai roka ba ginawa yayi a aljihun sa domin share musu hawaye.
Ilimi gishirin duniya inji masu magana, Sarki Ya yarda da wannan magana kuma ayyukan sa sun tabbatar da hakan,  ya gina islamiyya  da take daukan dalibai sama da dubu hudu a chikin Gombe
Wanan yasa mai martaba sarkin Gombe yasamu soyayyah mai tsanani daga mutane Gombe da duk mutumin dake zuwa kasar Gombe, zaku yadda dani in kun tuna yadda al’ummah tayi fitowan garin dango wajen Sarki bayan yadawo daga hawan durbur chikar Kaduna shekara Dari 
Ya mai martaba Sarki al’ummah duka suna  godia da yadda kake sauraron jama’a da sakakiyar fiskar Kauna da girmamawa 
Muna adu’a Kar Allah ya gajiyar dakai 
Allah yakara lafia da imani 
Allah yasa kabari sarkin Gombe Shehu yazama dausayi daga dausayin Aljannah  
Mungode Ranka yadade !

Leave a Reply

Your email address will not be published.