Shin ko Buhari zai daga hannun Ganduje a ziyarar yakin neman zabensa a Kano?

Shin ko Buhari zai daga hannun Ganduje a ziyarar yakin neman zabensa a Kano?
Ga tsokacin mutane 10 daga shafin BBC HAUSA na facebook, kowa yana fadin albarkacin bakin shi
1. Haka muke fata, domin daga hannu gamduje tamkar kawo rudani ne a jam’biyar APC
2. #Bbchausa mekukeci nabaka kezuba kuma mezai hana shugaba buhari daga hannun ganduje tunda shine dantakarar gwamnan jahar ajam’iyar #apc
3. Duk lallacewar gwamnan bauchi ma buhari ya daga hannun sa balenta ganduje.
4. To koma dai menene ai zamu gani yau din sannan daga hannun Ganduje da barin shi to duk ba shi bane abun mayar da hankali akai, fatan mu dai shine shugaba Buharin yaje Kanon lafiya ya koma Abuja lafiya.
5. Koshakka babu shugaba #buhari zaidaga hannun ganduje ajahar kano ganin yadda shine halattatcen dan takarar gwamnan jahar akarkashin tutar jam’iyar #apc
6. Agaskita babban kalu bale ne shugaba bahari ya daga hannun gwamna Abdullah umar ganduje a jihar kano, kuma kasantuwar hakanne iyan adawa zasu iya furucin cewa shugaba bahari ba dagaske yake ba kan batun yaki da cin hanci da rashawa a najeriya.
7. Ba dole ba, ai dole Kanwar naki, ai ita siyasa biki ce… Idan kaje na wasu dole azo naka, idan yayi mana Kyakkyawa yaga kyakkyawa a Akwatinsa, idan ya batawa Baba Ganduje dole yaga Mummuna,
8. Ziyarar yakin neman zabe da ake sa ran shugaba Buhari, zai kai jihar Kano, tabbas a kwai rikita rikita a cikinta ganin yadda wasu ke zargin gwamnan jahar da kar6ar rashawa.
9. za dai mu gani idan baba buhari da gaske yake Wajen yaki da cin hanci da rashawa, Gashi dai Kiri Kiri an nuna gwabnan mu na kano yana sunkome daloli 💵 ,yazama wajibi ga shugaba buhari yayi Allah wadai da wannan Hali na gwabna ganduje, bai kamata baba buhari ya daga hannun ganduje ba.
10. Indai BUHARI ya kuskura, yai gangancin daga hannun GANDUJE shikenan! Ta tabbata Buhari ne garkuwa mafakar barayin Nigeria. To daga nan kuma #karya yake yakuma da’awar yana yaqi da cin-hanci da rashawa. Snn sai mutunci da qiymarsa sun qara zubewa a idon Duniya. Mukuma #kanawa dama ba gidadawa bane, ba wanda ya’isa yasa mu zabi wanda zai ci-gaba da lalata mana jaha kowaye! Shi. ABBA KABIR YUSIF shine amsa. Abinda yaragewa Buhari yau a idon duniya, shine yaqara daga darajar kansa. Ko yaqarasa zubarwa da kansa qiyma ta hanyar daga hannun Barawon dala$.
Daga karshe muna fatan alkhairi akan zabe dake karatowa. 
#Arewagist.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published.