Uche Secondus yace akwai yaki matukar INEC tayi magudin zabe.

Uche Secondus shine shugaba jam’iyyar PDP na kasa yace akwai yaki a wannan kasan matukar akayi magudi a zaben shugaban kasa mai zuwa. 
Idan bamu manta ba jiya ne Alhaji Atiku Abubakar, dan kararar Shugaban kasa karkashin jam’iayyar PDP yaje jahar Asaba, Delta wato alhamis, yaje rally ne na neman shugabancin kasa, a wurin taron ne Uche Secondus yayi wannan jawabin kamar yadda Sahara Reporters suka kawo. 
Yace yau, muna jan kunne INEC, munsan cewa akwai mutanen kirki a cikinta, sannan kuma mun sani cewa Gwamnati mai ci tana tursasawa INEC kan suyi magudi a zabe mai zuwa,  yace ba komai suke nema ba sai yaki a kasan nan. 
Yace idan suna son zaman lafiya to kada su kuskura suyi magudi a zabe mai zuwa saboda kowa yana shirye da wannan zabe mai zuwa.
Sannan yace suna bada masu aikin tsaro shawara, munsan cewa akwai mutanen kirki wajen kare rayukan mutane da kuma dukiyoyi alhali wannan shine aikin su tun farko. 
Muna fatan zasu bi dokar kasa, ba kuma su take wannan doka ba kamar yadda shugaban kasa ke take doka ba. Su bi dokar kasa sannan su kasance tsaka-tsaki, amma idan suka ki ji suka sanya hannu suka biyewa INEC wajen magudin zabe, me suke nema kenan? 
Mutanen dake wurin suka ce “yaki” da karfin murya. 
Seconsus yace da wannan ne muke umurtan duk yan Nigeria su fito a wannan rana na zabe 16th February kwansu da kwarkwatansu domin su jefa kuri’a kuma su tsare akwatunan zaben su saboda dukkan kuri’un yan Nigeria za’a kirga.

Leave a Reply

Your email address will not be published.