YADDA ZA’A WARWARE SIHIRI–WANDA YA KASA KUSANTAR MATAR SA SABODA SIHIRI

YADDA ZA’A WARWARE SIHIRI–WANDA YA KASA KUSANTAR MATAR SA SABODA SIHIRI

A Tafsirin sa na ranar Juma’a 22-1-16 da yake gabatarwa a Masallacin Usman bn Affan dake gadon kaya, Dr Sani R/Lemo ya kawo bayanai da Ibn Baddal ya fada a Sharhin Bukhari kamar yadda ya ruwaito daga Wahb Ibn Munabbih.
.
Ibn Munabbih yace “Idan mutum yana son ya warware sihiri, ga yadda zai yi –sannan kuma yace wannan yana da matuqar amfani ga wanda aka masa sihiri ya kasa kusantar matarsa–sai a samu ganyen magarya kore (guda 7) sai a daka shi, sannan a zuba a ruwa, sai a karanta Kulhuwallahu da Falaki da Nasi da Ayatul Kursiyyu a tofa a ruwan, sai mutum ya sha sau 3 kuma ya yi wanka da shi, idan mutum ya yi haka to IN SHA ALLAHU Allah Zai tafiyar masa da duk abinda ke damunsa na Sihiri”.
.
Shi Ibn Munabbih asalinsa Bayahude ne ya Musulunta, yana daga cikin Tabi’ai, kuma daman kafin Musuluntar sa mutum ne mai Ilimi.
.
Wannar maganar tasa wasu Malamai da yawa suna kawo ta a littattafan su, kamar Ibn Qayyim ya kawota a Zaadul Ma’ad, Ibn Kathir ya kawota a Tafsirin sa, Ibn Baddal ya kawota a sharhin Bukhari.
.
Amma sai Mallam (Dr Sani) yace “Amma wannan gwaji ne, ba wai Hadisi ne daga Manzon Allah (s.a.w) ba, don haka idan mutum ya gwada aka dace shikenan”.
.
Kuma daman wasu Hausawan sunce asalin karmar “Magani” ai ana nufin  “Maa gani” ne, ma’ana za mu gwada mu gani.
.
Allah Ya sa mu dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published.