Anyi Nasarar Kammala Fassarar Litattafan PHYSICS, CHEMISTRY, MATHEMATICS zuwa yaren HAUSA.

Bayero University, Kano 
~Anyi Nasarar Kammala Fassarar Litattafan PHYSICS, CHEMISTRY, MATHEMATICS zuwa yaren HAUSA. 
~Cibiyar Bincike Kan Harsunan Nigeria da Fassara da Hikimomin Al’umma, Jami’ar Bayero, Kano. 
Wannan cibiya mai suna a sama tayi Nasarar buga da fassara Litattafan kimiyya guda takwas zuwa yaren Hausa saboda daliban Piramare, Karamar Sakandare (Junior) da kuma babbar Sakandare (Senior) Saboda dalibai ‘yan yankin Arwacin Nigeria. 
Farfesa Aliyu Mu’azu Director na wannan Cibiyar yace “Litattafan sune: 
1. Kimiyya da Fasaha don makarantun Firamare. Littafi na daya zuwa na uku. 
2. Lissafi don Kananan makarantun Sakandare. Littafi na daya zuwa na uku. 
3. Kyamistare (Chemistry) don manyan makarantun Sakandare. 
4. Fizis (Physics) don manyan makarantun Sakandare.
Wadannan sune Litattafan da aka Fassara zuwa yaren Hausa. 
Haka kuma wajen yin aikin wannan fassara Farfesa Mu’azu yace sunyi amfani ne da tsarin karantarwa na kasa (National Curriculum) tare da Taimakon abokan aikin su na Faculty of Science da kuma Faculty Of Education. 
Farfesa Mu’azu yace “Shawarar fassara wadannan Litattafan da kuma buga su yazo ne sakamakon kokarin da wannan cibiya takeyi na ganin ta bada nata gudun muwa wajen habaka ilimin zamani a yankin mu na Arewa ta hanyar koyarda ilimin da harshen uwa (Yaren mu/Hausa) dan haka wannan cibiya tayi amannar cewa koyo da koyarwa zai kasance mafi sauki da kuma fahimta matukar dai anayi ne da harshen Hausa (Mothers tongue) hakanan ya kara da cewa kaje kasashen da suka cigaba kagani, zakaga sirrin cigaban ilimin su shine koyar da shi da sukeyi da yaren su. A karshe Farfesa Mu’azu yace ” Cibiyar zatayi kokari wajen hada kai da hukumomin Jahohi dana tarayya dan tabbatar da cewa wadannan Litattafan ana amfani dasu a makarantun kasar” 
A jawabin sa mataimakin Shugaban Jami’ar Farfesa Muhammmad Yahuza Bello yace “Yayi alkawarin taimakawa duk wani cigaba da wannan cibiya ta kawo don habaka yaren Hausa (Mothers tongue) a arewacin Nigeria dama kasa baki daya. Haka kuma ya yabawa wannan Cibiya bisa wannan namijin kokari da tayi, yace wannan cigaba ne bawai ga Cibiyar kawai ba, har dama Jami’ar ta Bayero baki daya”
Itama a nata Bangaren Kungiyar Arewa Students Orientation Forum ta yabawa wannan cibiya bisa wannan Namijin Kokarin, kazalika daman Kungiyar tayita kiraye-kiraye akan yin wannan aikin na fassara, gashi Alhamdu_Lillah an fara samun Nasara. A karshe Kungiyar ta Arewa SOF tana kira ga daukacin hukumomin Jahohi dana tarayya da su amince da yin amfani da wadannan Litattafan a makarantun mu, dan haifar da kwararrun likitoci, injiniyoyi, da Sauran su.

17 thoughts on “Anyi Nasarar Kammala Fassarar Litattafan PHYSICS, CHEMISTRY, MATHEMATICS zuwa yaren HAUSA.

  1. Masha Allah. Fantastic. May almighty Allah continue to make things easy for us. May this big research work be beneficial to us. Jazakumullah chairman.

  2. Alhamdullilah godiya ta tarbbata ga allah, wannan shine babbar nasara da muke nema, dama ace professor's, da muke dasu haka za su rika yimana da mukai inda ba wanda zaikai kamal mu a duniya? Allah yakara girma da karfin kwakkwawa? Malan.

  3. We are thanks to almighty Allah the master,of the day of resurrecton.May God continous guide the nigerias and protect all the people of nigeria In a right.

Leave a Reply

Your email address will not be published.