ASUU Vs. FEDERAL GOVERNMENT

ASUU Vs. FEDERAL GOVERNMENT

~A YAU NE AKAYI ZAMA (MEETING) NA TARA TSAKANIN GWAMNATIN TARAYYA DA KUNGIYAR MALAMAN JAMI’O’I TA KASA (ASUU)

~ZA’A SAKE ZAMA RANAR 7TH FEBRUARY, 2019

A yau ne daya ga watan fabrairun Shekarar 2019 akayi zama (Meeting) na tara tsakanin gwamnatin tarayya da kuma Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa akan yajin aikin da kungiyar take ciki yanzu haka na wajen watanni uku, a daidai lokacin da kasar ke Fuskantar babban zabe na kasa baki daya, nan da kasa da kwana 15. A yayin zaman na yau tsakanin Kungiyar ta ASUU da kuma gwamnatin Tarayya ya samu wakilcin Chris Ngige ta bangaren gwamnati, da kuma President na Kungiyar ta ASUU, dan shawo kan matsalar wannan yajin aikin da yaki ci yaki cinyewa.

Idan baku manta ba Kungiyar ta ASUU ta tsunduma yajin aikin ne tun ranar 4th November, 2018, kusan watanni uku kenan da suka gabata.

Jim kadan bayan fitowa daga meeting din Ministan kwadagon da kuma President na Kungiyar ta ASUU sun tabbatar da cewa suna nan suna ta kokarin ganin an shawo kan matsalar yajin aikin. Saidai kuma Ministan Kwadagon Chris Ngige da kuma President na Kungiyar ta ASUU Prof.

Biodun Ogunyemi dukan su sunki su bada wani takamaiman bayani a lokacin da suke ganawa da manema kabaran jim kadan bayan fitowa meeting din. Sunce ne kawai, zasu sanar da al’umma abubuwan da ke faruwa amma ba yanzu ba, har sai anyi meeting na gaba (Na goma kenan), wato wanda za suyi nan da Sati daya, a ranar Alhamis Bakwai ga watan biyu. (7th February, 2019).

#arewasof
#arewagist.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published.