DAN SANDAN NIGERIA

DAN SANDAN NIGERIA. 
Nigeria Na Da Hukumomin jami’an Tsaro wanda Suke Kula Da sha’anin tsaro a ciki da wajen kasar.  Hukumar yan sanda a Nijeria hukuma ce mai Cin gashin kanta wanda take Karbar Umarni daga ofishin Shugaban Kasa Ko Kuma Manistan da Ya shafi Tasro Da Kuma Cikin gida.  
Hukumar tana Da rassa Da Dama Wanda Suke Gudanar Da Aiyukansu, Kamar Sashen Tsaro Da Tuntuba,  sashen Aikin Gaggawa,  Sashen Bincike Da Al’amuran Yau Da Kullum. sannan Akwai Sashen Manyan Laifuka.  
Kowanne Akwai Jami’in dake Kula Dasu Bisa Sahalewar Baban Jami’in Yansadan.  
Da yawa ana Wa yan-sandan Kallon mara Sa Kishin kasa Bisa Ga Yadda wasu Suka tasirantu Ta Karbar Cin hanci da rashawa, wasu kuma rashin kwarewa a aikin nasu.  Sai dea ba haka abin yake ba,  ko wanne aiki dan’adam zai, yana Bukatar Kulawa Ta Musamman Wacce Ta shafi Fannin Lahiyarsa, iyalansa Da kuma wal-walarsa. Shi yasa kasashen da suka ci gaba Kamar Kasar France sukan bawa Jami’an Tsaronsu Albashi Mafi Daraja na Biyu kan Sauran Aiyukan Kasar,  Haka Zalika a Amurka Albashin Jami’an Tsaro Shine Mafi Tsoka Kan Kowanne Bangare.  
Amma  A Kasata Nigeria ba haka abin yake ba.  A matsayin Albashin Dan Sanda na Kusa Na Shida Bisa ga Kowanne  Bangare Inda aka Fifita wani bangaren da bai kaisu ba muhimanci fiye da su.  
Tsohon Shugaban Kasa Umar Musa Yar’adu shine Wanda ya fara inganta misu albashinsu  da kuma Gyara musu hakokinsu a shekarar 2008, kawo zuwa yanzu babu gwamnatinda ta sake duba zuwa ga Wannan Yananin Albashin nasu da gyara shi.  
Muna Sane da yadda ake canza musu wajen aiki kamar yadda ake juya waina a tanda (wanda ke aiki a baga a jihar Barno An dauko shi an maida shi Ilela a jihar Sokoto). Tayaya ka ke tunanin yadda Zai gudanar da rayuwarsa bisa ga irin wannan canjin da akai masa.  
Ko kasan Dan Sandan Da yay Ritaya a matakin Mai ladabtarwa ko Matakin Sufeta ko kasan Haka (shekara Talatin da Biyar yana aiki), Kudin Fansho Dinsa bai Kai Miliyan Uku Ba.  
Ko kasan Idan Gidajen Da aka Tana ga Yan sanda (bariki)  in ya cika sai dea su fito su kama Haya.  
Ko kasan Idan Akai masa Canjin Wajen Aiki gari mai nisa ko kusa da kudinsa zai hada iyalansa su bar garin. 
Yakamata Mu fahimta Cewa Amfanin dan sanda A Nigeria Cewa muhimancin sa yafiye tunanin mu,  kamar yadda in kai tunani kai kadai ko kukayi a jumlace kaga Yau babu yan-sanda ko kuma sunyi yajin aiki, ya ke tunanin Kasar zatakasance.  
Muyi Musu Addu’ar Zaman Lafiya da samun kulawa mafi ingancin dan Warware matsalolin rayuwarsu ta Yau da kullum. 
Salim Sani shehu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.