HAKKIN MAKWAFTAKA…

HAKKIN MAKWAFTAKA…
An ruwaito athari ingantacce cewa, 
Daya daga cikin magabata ya kasance yana da makwafci wanda suke ga gida da gida,
Ya kasance agidan wannan makwafcin akwai wata bishiya me yelwataccen inuwa, har akan zauna a inuwan don a huta.
Rannan sai wannan makwafcin yaji labarin ai abokinshin cen ya sanya wannan gida a kasuwa zai sayar don ya samu ya biya bashi ya ake binshi.
Bayan yaji labari saiya bari har saida aka taya gidan, sai ya kira wannan makwafcin nashi ya dauki  kudin gidan ya bashi  yace yayi hakuri karya sayar da wannan gida.
DALILAN DA SUKA SA YA BASHI KUDIN WANNAN GIDA…
1-Yayi hakanne don gudun kar in ya bari ya sayar da wannan gida zai rasa inuwan da xaina fakewa.
3-yaji tsoron kar abokin zamansa ya tagayyara ta hanyar rasa muhallinsa.
3-Kuma yana tsoron kar Allah ya kamashi akan bai taimaka wa makwafcinsa ba ayayin da matsala (bashi) ya addabeshi alhalin yana da daman hakan.
Intahah
Kaji bayi na kwarai, ba irin na yanzu masu neman kota halin qaqa sai sun saye gidajen makwaftansu don su mayar da nasu unguwa duga ba, kuma  ba ruwansu da tunanin wani irin mawuyacin hali wancen zai shiga ba!!!
Allah ka ganar dasu damu baki daya.
 Amin 
#Repost

Leave a Reply

Your email address will not be published.