DUBUN DUBATAR MUTANE SUN AMSA KIRAN SHEIKH BALA LAU NA ZABAR PMB

DUBUN DUBATAR MUTANE SUN AMSA KIRAN SHEIKH BALA LAU NA ZABAR PMB

Kungiyar kiristoci ta (CAN) ta dade tana daukar matsaya akan abunda ya shafi siyasar da suke gani itace maslaha a wurin su,wanda hakan ba laifi bane a tsarin ‘yanci na najeriya.

An dade ana yiwa musulmi na Arewa wayo sai a rinka cewa wai babu ruwan malamai da sarakuna da siyasa amma sai abu ya lalace azo wurin Malamai akan suyi addua.

Don haka mutanen najeriya musamman musulmi sun amsa kiran sheikh Abdullah bala lau don dukkan rahoton da muke samu daga malamai da aka tura don wayar da kan mutane akan Wannan matsaya an samu mika wuya da mubaya’a wacce ta bada mamaki.

Kuma mutane masu nufin sharri ga wannan kungiyar suna ta cewa an baiwa kungiyar jibwis Nigeria kudi to kowa ya sani raba kudi baya cikin tsarin Muhammadu Buhari don haka tallan baba buhari yiwa kai ne.

Allah ya bamu sa’a akan dukkan abunda muka sanya a gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.