Google+ suna dab da rufe manhajarsu, wanda ya ajiye abu a ciki yaje ya sauke.

Google+ zasu rufe kayan su saboda wasu dalilai nasu
Kamar yadda suka ce: sun sanar tun a watan goma sha biyu wato December cewa wasu  rufe wannan Google+ a watan hudu mai zuwa wato watan April. 
Sunce zasu rufe ne saboda dalili kamar haka:
1. Karancin masu amfani da Google+ 
2. Matsalolin sarrafa wannan google+ domin anfanuwar abokan cinikayya.
Sukace suna godiya ga jama’a da suka kasance dasu da wannan tsawon lokacin da kuma mataki na gaba, wanda ya hada da yadda mutum zai sauke hotunanshi da kuma sauran kayayyakin shi da ya ajiye. 
A ranar 2nd April ne zasu rufe wannan Google+ da duk wasu shafuka(pages) na Google+ wanda mutum ya kirkira duk zasu rufe su. 
Sukace zasu fara goge hotuna, video daga Google+ na ma’ajiyar mutum wato archive, da kuma shafuka da, suka ce daga yanzu mutum zai iya sauke duk abinda ya ajiye akan Google+ kafin watan hudu,  amma hotuna da video da mutum yayi backup dinsu bazasu taba ba. 
Tsarin goge abubuwa da mutane dake an Google+ accounts, sai shafuka sai kuma ma’ajiyar hotuna zai dauki wasu watanni, abubuwa kuma zasu kasance a wannan lokacin. 
Suka ce daga ran 4th February ne mutum bazai iya sake bude sabon account na Google+ ba ko kuma shafuka da sauransu. 
Suka ce duk mai son sauke abubuwanshi to ya fara tun farkon watan uku wato March 2019.
Idan kuma kana shiga wasu shafuka a ranar giza da Google+ ne da madanni(button) to wannan madannin zai dena aiki a satuka masu zuwa, amma za’a iya canza shi da wani, sannan duk inda dama kake shiga da Google+ yanzu zaka iya shiga da google account dinka. 
Idan kana amfani da Google+ ne wajen yin tsokaci(comment) akan wasu shafukan ka, to wannan tsarin za’a cire shi daga Blogger ran 4th February, a wasu shafukan kuma sai watan March 7th. Sannan duk wani comments da ka taba yi da Google+ za’a goge shi daga ran 2nd April 2019.
Idan kuma kana amfani da G suite ne, Google+ account dinka baza’a goge shi ba, amma ka tuntubi ma’aikatar G suite domin karin bayani. 
#Abu Abdirrahman Kaltungo 
#CEO Arewagist.com.ng
2nd February, 2019

Leave a Reply

Your email address will not be published.