MUHAWARAR ‘YAN TAKARAR GWAMNAN KANO TA #BBCHAUSA.

MUHAWARAR ‘YAN TAKARAR GWAMNAN KANO TA #BBCHAUSA.

Na kalli wannan muhawara har zuwa karshenta bisa lura da bayanan da kowa ya yi a cikinsu sai na yi musu matsayi guda hudu kamar haka:

1. Idan kana so ka samu Gwamna ‘dan boko mai hankali to ka zabi Engr. Abba Kabir Yusuf

2. Idan kuma Gwamna matashi mai karsashi da hamasa (samartaka) wanda samari za su juya gwamnati to ka zabi Cmrd. Mustapha Getso.

3. Idan kuma Gwamna Kake so wanda zai maida hankali akan mata da kudurorin mata to ka zabi Hajia Maimuna Muhammadu.

4. Idan kuma so kake ka samu dattijon Gwamna wanda zai yi abin da ya kamata a lokacin da ya kamata sai ka zabi Malam Salihu Sagir Takai.

Allah ka zaba mana abin da ya fi alkhairi wanda ze amfane mu ya amfani Musulunci. Ameen

Leave a Reply

Your email address will not be published.