AHMADU BELLO UNIVERSITY ZARIA ABU ZARIA

Musan Tsangayoyin Mu

-Faculty Of Law

 AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA (ABU)

Ko zan iya saka darasin Hausa acikin Combination dina na Jamb, Idan inaso na karanta Shari’ah Law a ABU ?

Tabbas darasin Hausa yana daya daga cikin darusan da Jami’ar ta Ahmadu Bello dake zaria take la’akari dashi ga duk wani dalibin da yakeso ya karanta Shari’ah Law a Jami’ar.
A rubutun mu na baya-bayan nan mun bayyana cewa ba’a saka Hausa a Jamb Combination na law, to amma bayan tuntuba da neman karin Bayani mun samu tabbacin cewa zaka iya saka hausar, indai a ABU din ne, kuma a Shari’ah Law, hasalima suna la’ akari dashi sosai. Dan haka Ehh zaka iya sakawa.

Shari’ah Law ko Islamic Law yana daya daga cikin bangarorin da Faculty Of law na ABU sukeyi. Kuma Course ne mai matukar kyau da ban Sha’awa

SANARWA:-
Amma fa ku sani a Shari’ah law ne kawai suke amsar hausa din, idan ba Shari’ah bane to basa karba.

Allah ya taimaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published.