Musan tsangayoyinmu kashi na 02

Musan Tsangayoyin mu

Kashi Na 02

(13-01-2019)

1- Faculty Of Law:-

Abubuwan da zamu tattauna a wannan tsangayar sune:-

-Menene Law

-Wanene Lauya

-Yaya daliban Law suke

-Career Job Opportunities

-Abubuwan da ake bukata ga wanda yakeso ya karanta Law

-Abunda kowace Jami’a take bukata

-Rabe-Raben Law da Jami’o’in da suke yin su

-Menene Law ?

The terms “LAW” can be defined as a rule of conduct established and enforced by the authority of a given school, company community, State, nation etc.

-Wanene lauya ?

A Lawyer is a person taught to practice law i.e. someone who studies law in school (University)

-Yaya daliban Law suke

Tsangayar Nazari, ko kuma koyon karatun dokoki (Faculty Of law) tsangayace mai cike da farin jini agun dalibai dama iyayen su a kasata Nigeria. Tsangayace da ake rige-rige wurin neman shigar ta.
Haka suma daliban wannan tsangaya (Faculty) suna bambanta kansu da sauran dalibai, saboda su dalibai ne masu ji da kansu, hasalima suna ganin duk wani dalibi indai ba law yakeyi ba to kamar kawai bama boko yakeyi ba, suna jin cewa a jami’a su kadai ne dalibai, duk sauran daliban kawai sun rako dalibai ne. To amma a hakikanin gaskiya ba haka abun yake ba, kawai dai muna fadin halayen su ne da dabi’ar su.
Kazalika daliban law dalibai ne da sukeda kwarewa wajen iya tsara magana, kana kuma sun kware wajen turanci, idan sukaga dama zasu rika yimaka magana da turancin da har su gama bakama san ina suka dosa ba. Haka kuma dalibai ne da kayan sawar su ya bambanta dana kowanne dalibi, kai hasalima ba kowanne kaya ne ake sakawa a shiga Faculty din dashi ba. (Wani Friend dina ya taba shiga Faculty din zaiyi karatu da wando Crazy, sai suka koreshi, lecturers din suke gaya masa wannan Faculty din ba irin sauran faculties bane) Wannan sune daliban FACULTY OF LAW.

-Career Job Opportunities:-

Idan muka koma ta dayan bangare zamuga cewa Law ba kwas bane da yake bukatar sai anyi maka bayanin aikin me zakayi idan ka gama, to amma duk da haka zamuyi bayanin irin wuraren da wanda yayi Degree a law din zai iya yin aiki.

Zamu Cigaba Insha’Allh.

Leave a Reply

Your email address will not be published.