Musan tsangayoyinmu kashi na 04

Musan Tsangayoyin Mu

Kashi Na 04

(15-01-2019)

FACULTY OF LAW

-Abubuwan da ake bukata ga wanda yakeso ya karanta Law

Akwai Abubuwan da ake bukata ga duk wanda yakeso ya karanta law, wanda abubuwan sun kasu zuwa gida biyu

1- Abubuwan da ake bukata a Dabi’ance

-Dole ka zama mai kaifin Kwa-kwalwa da tunane, da iya hadda (Memorization) na abubuwa. Saboda Law Course ne da yake da bukatar haddace abubuwa kamar Su Cases, Chapters, Sections na Irin su Constitution, penal Code, Criminal Code, Criminal Procedure Code da sauran su.

-Dole ka zama maras tsoro, mai karfin hali da juriya, ya zama koda mutanen duniya aka tara maka zaka iya tashi gaban su ka gabatar da hujjojinka

-Dole ka tabbata ka iya turanci Sosai, ko kuma zaka iyayi gwargwadon iko, Saboda tabbas law sai da turanci.

2- Abubuwan da ake bukata a ilimance:-

SSCE:
-Dole ya zama akalla kanada Credit biyar a SSCE dinka (Waec/Neco) gasu kamar haka:-

• English language

• Government

• Literature in English

• Mathematic (Amma wasu Jami’o’in ko bakaci Maths ba a SSCE dinka suna iya baka Admission)

• Economics

• Islamic Studies ko Arabic (Amma ga wanda yakeso ya karanta Shari’ah law, ko kuma Common and Islamic Law)

UTME/JAMB

-COMBINATION:-

• English Language

• Government

• Literature in English

• Arabic Ko Islamic studies
(Amma ga wanda yakeso ya karanta Islamic Law, ko Common and Islamic Law, kokuma Private and Islamic Law)

KARIN BAYANI:-
Dayawa wasu dalibai suna daukar cewa wai tunda Shari’ah law zasuyi to zasu saka darasin Hausa acikin jerin darussan da zasuyi a jamb, to gaskiya wannan ba daidai bane kar kazo garin neman sauki kuma ka jazawa kanka rasa admission, dan kuwa babu Jami’ar da zaka saka ma Hausa a law kuma ta baka Admission.

Karatun Lauya a Nigeria Shekara biyar ne ga wadanda suka fara ta hanyar Jamb, masu Direct Entry kuma Shekara hudu ne, Sai kuma Shekara daya da zakayi a Makarantar koyon aikin lauya (Law School) Sai kuma Shekara daya ta bautar kasa (NYSC) kenan kafin mutum ya zama cikakken lauya Sai ya Share Shekara 7 hade da Shekara dayar bautar Kasa, idan da Jamb ne ya fara karatun, idan kuma D.E ne zai share Shekara 6 ne hade da Shekara dayar bautar Kasan shi

Zamu Cigaba Insha’Allh.

Leave a Reply

Your email address will not be published.