[Jamb] Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB? Kashi na 1

Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB?

Kashi Na 1
( 05-02-2019)

•Shi Ban iya Computer Bane?

•Shin Ban iya Karatun Bane?

•Mecece Matsalar?

Amsar Wannan Tambayar Tana Kunshe Ne a Abunda ka iya Hararowa Kai da kanka kokuma Wani wanda Yafahimci Hakikanin Matsalar ka.

Kungiyar Asof. Tadamu Matukar Damuwa Wajen Ganin Yawan Daliban Arewa Dasuke Faduwa
 Jarrabawar JAMB,

 Dayawa Daga Cikin Su da Asof. Ta zanta Dasu wasu Sunyi Jarrabawar JAMB so Biyu wasu So Uku wani Ma da Asof. Ta Tattauna Dashi So biyar Yayi JAMB beci Ba!

a ina Matsalar Take?

1• “JAMB ba Jarrabawa ba”

 Wannan Wani Kallo ne Da Dalibai Sukeyi Wa JAMB Wato Suna ganin cewar Tunda Jarrabawar a Computer Akeyin Ta,

 kuma obj Ce Wato Zabi katika, Basai Sunyi karatu ba Ai JAMB Sa’a Ce!

 Matakin Farko Kenan Dayake Kada Daliban Mu Na Arewa.

•Hanyar Gyara Matsalar Farko:-
Ya Dan Uwa Kasani Cewa Jarrabawar JAMB Kamar kowacce Jarrabawa Ce Malamai ne a Kowanne Bangare Suke Shirya Tambayoyin, kuma Computer tana iya Fahimtar Cewa ka Amsa Tambaya Dai Dai ko Akasin Hakan,

Kamar Yanda Ka’amince Cewa Computer tana iya Ganowa idan kudin wayar ka Yakare ko Data

Shin kayi Tunani wayar ka Zatayi Kira idan babu Kudi?
 Meyasa?  Computer Datake Lura da Wannan Bangare Tagano baka da Kudi Kamar Yanda computer take iya Gano Amsar ka shin Dai Dai ce Ko A’a a Lokacin  Dakake Amsa Tambayoyin JAMB.

 Yazama Wajibi Muyi karatu Kamar Yanda Mukeyi a kan kowacce Jarrabawa, Bari Made muyi Karatun Sama da Irin Wanda Mukeyi a Sauran Jarrrabawa

Sbd Kamar Yanda kuka Sani JAMB So Daya Akeyin ta a Shekara.

•Shawarwari Akan Wannan Batu:-

1•>Pass Questions Paper
2•>JAMB 2019 Syllabus
3•> Littafan Karatu
4•>Lokaci Na Musamman
5•>Bibiyar Malamai

1•>
Idan Muka Duba Abu Nafarko Zamuga Tabbas Bekamata kashiga Dakin Jarrabawar JAMB ba Batare da Kasan Tsari da yanayin Yanda Ake Shirya Tambayoyin ba, Mallakar Pass Q Zai Taimaka Maka Matuka Wajen Fahimtar Abubuwa.

2•>
Syllabus kuwa Dashine Zaka San shin Me zaka Karanta?
Misali Kai Dalibi Ne da Zakayi Chemistry Ko Economic shin Me zaka karanta Tunda Chemistry Yanada Fadi Sosai, Idan kasamu syllabus Tabbas zaka San inda Yakamata kakaranta.

3•>
Littafin Karatu Shine Jigon Kowanne karatu idan baka da Littafin karatu Tamkar Manomi NE Dayaje Gona babu Fatanya, Akwai Littafan da JAMB Dakanta Take bada Shawarwarin Akalla Mutum Ya Sayi Daya a Kowanne subject dazeyi a JAMB.

4•>
Yazama wajibi ka Kebance Lokaci Na Musamman Domin Yin karatu Cikin Nutsuwa Hakan Zai baka Damar Fahimtar Komai.

5•>
Ba Wai ko Yaushe Kai Kadai zakake karatu ba Komun Sanin ka da ilimin ka baka Kai kowa ba, Yakama ta Kadinga Bibiyar Malamai ko Abokan Karatun ka Domin kakara Fahimtar Abubuwa Dayawa.

Kungiyar Arewa Students Orientation Forum.
Tadaura Damarar Samar Da Sauyi Sosai a Wannan Shekarar Ta Bangaren Samun Dalibai Masu Yawa dazasu Ci Jarrabawar da Taimakon Allah.

Zamu Cigaba insha Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published.