A ko wane lokaci ASUU zata iya Ci gaba da yajin aikin ta

~A ko wane lokaci ASUU zata iya Ci gaba da yajin aikin ta

~Ba fa wai Mun jaye yajin aikin bane gaba daya, mun dai dakatar ne

~Idan gwamnatin Tarayya ta kasa cika yarjejeniyar da aka cimma zamu cigaba da yajin aikin da yafi na farko

Gamammiyar Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa a Nigeria ASUU a takaice ta  bayyana cewa zata iya ci gaba da yajin aikin da ta share tsawon wata uku da kwana uku tana yi matukar dai gwamnatin tarayya ta kasa cika alkawura da yarjejeniyar da suka cimma a tsakanin su. Kamar yadda ta bayyana a Shafinta na twitter.
A Jawabin da Shugaban Kungiyar na Kasa Prof. Biodun Ogunyemi ya fitar wanda Gidan BBCHausa da jaridar Vanguard da Premiumtimes suka buga Professor Biodun din yace “dalilin da yasa Kungiyar ta dakatar da yajin aikin shine; akwai manyan bukatu takwas da muka gabatar inda muka cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya akan guda hudu, yayin da kuma muke jiran ta duba sauran hudun”

Professor Biodun din yace Kungiyar ta ASUU za ta koma yajin aiki idan har gwamnatin Tarayya ta ki mutunta yarjejeniyar 2017 da suka sanya wa hannu.

Bukatocin da Kungiyar ta ASUU ta nema guda takwas ne, kuma mun kasa su zuwa gida biyu, hudu daga ciki an cimma matsaya, hudu kuma ba’a cimma matsaya ba.

Wadanda aka cimma matsaya a kan su, sune:-

1. Bukatar a tabbatar da kamfanin fansho mai zaman kansa da zai kula da kudaden fansho na malaman jami’oi wanda tuni aka samu lasisin kamfanin da ake kira NuPemco.

Shugaban Kungiyar ta ASUU yace an shafe shekara 10 ana tattauna batun amma an kasa aiwatarwa.

2. Biyan kudaden albashin da malaman jami’oi 20 Suke bin bashi.

3. Samar da hurumi da za a hada kai tsakanin kungiyar ta ASUU da gwamnoni wadanda ya kamata su samar da kudi musamman domin tafiyar da jamo’in jihohi. Shugaban Kungiyar ta ASUU yace an kirkiro tsarin tare da tabbatar da shi.

4. Kara tabbatar da bangarorin da za su ci gaba da tattaunawa da juna tsakanin bangaren kungiyar ta ASUU da kuma Bangaren gwamnatin tarayya domin samun karin haske kan inda gwamnati ta dosa.

Wadannan sune bukatocin guda hudu da aka cimma yarjejeniya akai.

Wadanda kuma ba’a cimma wata yarjejeniya ba sune:-

1. Kwamitin kai ziyara ga dukkanin jami’oin tarayya

2. Biyan alawus-alawus din malaman jami’a

3. Biyan kudaden alawus na malaman jami’ar Ilorin wadanda har yanzu suke bin bashi

4. Kudaden jami’oi da suke jiran gwamnati ta saki, Naira biliyan 25 tsakanin watan Maris zuwa Afrilun 2019.

Wannan sune bukatocin nasu guda takwas, jimilla.

Leave a Reply

Your email address will not be published.