Gwamnatin tarayya kawai ake jira ta amince domin a fara amfani da Fassarar Physics, Chemistry, Biology dss na hausa.

-Fassara Litattafan Physics da Chemistry zuwa yaren Hausa

-Gwamnatin Tarayya kawai muke Jira ta amince

Bayero University, Kano.

Kusan sati biyu da suka gabata mun kawo muku labarin Fassara Litattafan kimiyya da Fasaha da wata Cibiya dake Jami’ar Bayero dake Kano tayi, to dalibai sun matsa da dokin sanin ta yaya za’ayi su samu wadannan Litattafan. Hakan ne yasa Kungiyar ta ziyarci Cibiyar da Sanyin Safiyar yau inda tayi Nasarar tattaunawa da Sakataren Cibiyar dan Sanin inda za’a iya samun wadannan Litattafan.

Sakataren ya fara bayani da cewa “wannan Fassara ba munyita bane kara zube, ba kuma wai manufar mu shine kowa yaga dama yaje kasuwa ya siya ya karanta ba a karan kanshi, a’a manufar mu shine mu nuna ma gwamnatin tarayya cewa babu darasin da baza’a iya koyar dashi da Hausa ba, Sannan kuma sai mu nemi amincewar ta akan koyar da wadannan darussa cikin harshen hausa aduk fadin Jihohin mu na Arewa guda 19, ta hanyar amfani da wadannan darussa da muka Fassara.

Saboda haka mun fassara Litattafan kuma mun buga mun kaima Mataimakin Shugaban Jami’ar Farfesa Muhammmad Yahuza Bello kuma ya amince da aikin, kana kuma mun gayyato hukumomin ilimi daban daban dan su duba aikin, sun duba kuma sun amince, saboda munyi aikin ne daidai da minhajin koyarwa na kasar,

yanzu gwamnatin Tarayya kawai muke jira idan ta amince ayi amfani da Litattafan a makarantu Shikenan sai kuma mu nemi gwamnatin Jihohi su kuma su samar da kudaden da za’a buga Litattafan a raba su a kowace Makaranta tun daga kan firamare har Sakandare. Haka kuma ya kara da cewa munaso arika amfani dasu ne har a Jami’o’i, ya zama da Hausa za’a koyar dasu, Saboda Litattafan da turanci aka yisu, kuma turanci yare ne, muma hausar tamu yare ne, to mu mai zai hana muma mu rika koyarwa da namu yaren ? Inji Shi.

Idan kaje wasu kasashe bazaka fara karatu ba dole sai ka koyi yaren su. Dan haka ina mai tabbatar maka babu wani darasin da baza’a iya koyar dashi da Hausa ba.
Da jin haka, Kungiyar tayi mashi tambaya akan cewa to idan har gwamnatin Tarayya tace bata yarda ayi amfani dasu ba to yaya zakuyi kena?

Sai yace “Idan bata yarda ba, to kaga babu yadda zamuyi kawai zamu buga su ne a rika siyarwa duk mai bukata sai yaje ya siya ya karanta kashin kansa, amma mu hakan ba shine manufar mu ba, manufar mu shine gwamnatin ta Amince ayi amfani dasu a makarantun mu, kama tun daga Firamare har zuwa Jami’a. Inji Shi.
Hakanan kuma yace Sun Kaima Sarkin Kano Muhammmad sanusi na biyu, kwafin Litattafan saboda shima ya jajirce da bada gudun muwa wajen ganin anyi wannan Fassarar.

Wannan Shine takaitaccen tattaunawar Kungiyar dashi akan wadannan Litattafan.

Dan haka muna kira ga duk wani mai ruwa da tsaki a gwamnati da su dage kai da fata wajen ganin gwamnatin ta amince da wannan bukatar.
A karshe ASOF zata Cigaba da bibiyar wannan batun Insha’Allh.

Leave a Reply

Your email address will not be published.