KURI’UN MU YANCIN MU //01

KURI’UN MU YANCIN MU //01
.
A Zabukan shekarar 2019 (dubu biyu da sha tara) Rubutun ilmantar da dan kasa mai kada kuri’a.
.
● GABATARWA: 2019 wata shekarar da za’a sake yin Zabe ta zagayo. Muhimmancin Zabe shine ya taimake mu wajen yanke hukunci akan wadanda zasu mulke mu a matakan tarayya da jaha da kuma wadanda zasu wakilce mu a majalisar wakilai ta kasa da ta dattawa da kuma majalisun wakilan mu na jihohi.
.
● Bai kamata Zabe ya zama dalili na yin fadan addini ko kabilanci a tsakanin mu ba.
.
ZABUKAN 2019, ABUNDA AKE TSAMMANI DAGA GARE KA A MATSAYINKA NA DAN KASA MUSULMI:
.
● A matsayinka na musulmi, kasan cewa wajibin ka ne kayi biyayya ga dokokin ALLAH a kowane lokaci cikin komai har da harkan Zabe.
.
● Saboda haka akwai abubuwa da ya zama wajibi ka aikata da kuma wasu wanda bai kamata ka aikata ba, a matsayinka na dan kasa musulmi acikin wannan Zabukan 2019 da ke gabatarwa.
.
ABUBUWAN DA SUKA ZAMA WAJIBI KA AIKATA A MATSAYINKA NA DAN KASA MUSULMI:
.
● Ya kamata ka fita Kada kuri’arka saboda alhakinka ne na dan kasa nagari.
.
● Kayi biyayya ga dokokin fa hukumar Zabe ta kasa ta gindaya akan kada kuri’a.
.
Acikin Alqur’ani mai girma ALLAH (SWT) Yace:
.
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَأُولِي الْأَمْرِ مِنكُمْ ۖ فَإِن تَنَازَعْتُمْ فِي شَيْءٍ فَرُدُّوهُ إِلَى اللَّهِ وَالرَّسُولِ إِن كُنتُمْ تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ ۚ ذَٰلِكَ خَيْرٌ وَأَحْسَنُ تَأْوِيلًا
.
“Yã kũ waɗanda suka yiĩmãni! Ku yi ɗã’a ga ALLAH, kuma ku yi ɗã’a ga ManzonSa, da ma’abũta al’amari daga cikinku. Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga ALLAH da ManzonSa idan kun kasance kunã ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. wannan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara.”  [Q-4;59]
.
● Ka tabbatar ka kada kuri’arka a bisa lamarinka. Ka yanke hukunci akan wanda zuciyarka ta natsu dashi kuma kake ganin zai iya kaika ga gacci wajen kwankwadar romon damokaradiya.
.
Ka kuma Karanci ko wane dan takara da kyau kafin lokacin Zabe. Kayi bincike akan shirye-shiryen su. Ka zama mai wayo wajen zaben dan takara. Kada kayi Zabe akan son kai saboda kawai dan takara addininku ko kabilarku ba daya da shi/ita ba. Ka zabi wanda kake tunanin zai taimakawa jama’a kuma ya inganta rayuwar mafi rinjayen kyan najeriya.
.
Acikin Alqur’ani mai girma ALLAH (SWT) Yace:
.
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُونُوا قَوَّامِينَ بِالْقِسْطِ شُهَدَاءَ لِلَّهِ وَلَوْ عَلَىٰ أَنفُسِكُمْ أَوِ الْوَالِدَيْنِ وَالْأَقْرَبِينَ ۚ إِن يَكُنْ غَنِيًّا أَوْ فَقِيرًا فَاللَّهُ أَوْلَىٰ بِهِمَا ۖ فَلَا تَتَّبِعُوا الْهَوَىٰ أَن تَعْدِلُوا ۚ وَإِن تَلْوُوا أَوْ تُعْرِضُوا فَإِنَّ اللَّهَ كَانَ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرًا
.
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayuwa da ãdalci, mãsu shaida sabõda ALLAH, kuma kõ dã a kanku ne kõ kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida kõ a kansa) ya kasance mawadãci kõ matalauci, to, ALLAH ne Mafi cancanta da al’amarinsu. Sabõda haka, kada ku bĩbiyi son zũciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, kõ kuwa kuka kau da kai, to lalle ne ALLAH Yã kasance Masani ga abin da kuke aikatãwa.”  [Q-4;135]
.
● Ka girmama hakkin sauran masu kada kuri’arsu su zabi wanda suke so su zaba koda ba shine dan takarar da kake so ba. Taka rawa acikin tsare-tsaren siyasa hakki ne kuma wajibi ne akan dukkan ‘Yan kasa wanda suka kai shekarun kada kuri’a daga dukkan addinai da kabilu.
.
Acikin Alqur’ani mai girma ALLAH (SWT) Yace:
.
يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنَّا خَلَقْنَاكُم مِّن ذَكَرٍ وَأُنثَىٰ وَجَعَلْنَاكُمْ شُعُوبًا وَقَبَائِلَ لِتَعَارَفُوا ۚ إِنَّ أَكْرَمَكُمْ عِندَ اللَّهِ أَتْقَاكُمْ ۚ إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرٌ
.
Yã kũ mutãne! Lalle ne Mũ, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangõgi da kabĩlõli, dõmin ku san jũna. Lalle mafĩfĩcinku daraja a wurin Allah, (shĩ ne) wanda yake mafĩfĩcinku a taƙawa. Lalle nẽ ALLAH Masani ne, Mai ƙididdigẽwa.” [Q-49;13]
.
#OurVoteOurPower.
#CommunityLifeProject(CLP)
#Nigeria2019.

Leave a Reply

Your email address will not be published.