Kwankwaso da Malaman Ahlussunnah . Mene Gaskiyar Magana?

Kwankwaso da Malaman Ahlussunnah . Mene Gaskiyar Magana?

Da farko inason kowa ya bincika maganata a duk inda zai bincika domin tabbatar da sahihancinta.

1: Kwankwaso shine ya fara qaddamar da shari’ar musulunci a kano.

2: kwankwaso shine ya fara kafa hukumar Hisba a fadin kano.

3:kwankwaso shine ya fara bawa maluman Ahlussannah manyan kujeru a Gwamnati.

4: Kwankwaso shine yabawa Mal Aminu Ibrahim Daurawa Commander na Hisbah Kano state.

5: Kwankwaso shi kaɗai ne Gwamna a fadin  Nigeria musulmin daya kiyaye mutumcin matarsa a musulunce, baa ganinta baa ganin hotonta kuma batada ruwa acikin mulki.

6: Kwankwaso shine Gwamnan daya haɗakai da sarkin kano sukaƙi yadda yabada goyon baya agina babbar coci acikin jami’ar Bayero ta kano.

7: Kwankwaso shine wanda ya sulhunta rigimar data kunno kai tsakanin yan Qadiriya da Ahlussannah a kano.

Yanzu semu kalli menene ya jawo kwankwaso yayi maganar da yayi kuma da suwa yake?

Abdallah Saleh Pakistan da tawagarsa sun cinye kudin ginin masallaci dana islamiyya a unguwar sabuwar gandu, Committee na Masallacin suka shigar dasu qara a kotu. Kotu ta buqaci abdallah Pakistan ya dawo da kudin, seyace ai daman rancen kudin yayi kuma yanzu bashida kudin, Se Ganduje yayi qundunbala ya bawa Saleh pakistan kudin dazasu biya a kotu har da chanji. Baa dade ba se bidiyon Ganduje na amsar cin hanci ya bayyana. Mezai faru se kawai Saleh Pakistan ya kwashi mutanensa suka tafi gidan Gwamnati wajen Ganduje aka nunasu a gidan tabaijin Pakistan yana cewa sunzo ne su bayyanawa ganduje goyon bayansu gareshi kuma bidiyo da aka nunashi yana amsar daloli basu yadda dashi ba. Daga nan se Pakistan da irinsa a kano suka fara hawa kan mumbari suna yiwa Ganduje kamfen har seda takai a masallacin Gwammaja Malam Lawal Gwauran Maje yana cewa su Ganduje yayi musu riga da wando ya basu shinkafa sabida haka mutane su zabeshi (akan mumbarin Khutba ta jumaa).

Yanzu seka yanke hukunchi, shin ka yadda akwai malamai mabiya annabawa kuma akwai Malamai mabiya Dollars?

Leave a Reply

Your email address will not be published.