YAYEN ‘YAN AGAJI MATA KARO NA FARKO

YAYEN ‘YAN AGAJI MATA KARO NA FARKO

Via: Abu Bilal Dan Majema

Gundumar Kabala Costain ta yaye Yan Agaji Mata Karo na farko wato Nisa’us Sunnah a yau 09/02/2019.

Sheikh Aminu Ibrahim Sautussunnah ya yi jawabai masu tsawo Kan muhimmancin Mata Yan Agaji a Musulunce da gudumawar da suke badawa a cikin al’umma.

Matan da aka yaye sun gabatar da aikin Agaji a aikace Don nuna ma mahalatta taro yadda suka shafe wata shida suna koyon aikin.

Nisa’us Sunnah na gundumar sun karrama Malaman da suka koyar dasu aikin Agajin na tsawon wata shida tare da sauran Wanda suka bada Gudumawa kan kammaluwar karatun su, Malaman Nasu sune Mal. Abubakar Muhammad, Mal. Hamza Usman, Mal. Aminu Zubairu da Mal. Kamal Abubakar, Alh. Salisu Usman da Mal. Adamu Abdullahi Shugaban Kabala Costain.

Dr. Hadiza Balarabe (Dep. Governor Kaduna State) ta halacci taron ta kuma bada gudumawar ta na #50, 000 tare da littafin Rubutu da atamfuan, da sauran Yan Siyasa da suka hada da Hon. Isah Yusuf Haladu (Dan Maryam) da ya bada #5000 da Dai sauran su duk sun bada gudumawar su.

Hamza Usman
FAG OF JIBWIS SOCIAL MEDIA KABALA COSTAIN DETACHMENT, KADUNA NORTH DIVISION KADUNA STATE
05th Jumada Ath-Thani 1440 AH
*09th February 2019 CE*

Leave a Reply

Your email address will not be published.