[[Zaben 2019]] ‘Yan Social Media Sunyi taro a Kano

[[Zaben 2019]] ‘Yan Social Media Sunyi taro a Kano

A ranar litinin 11-02-2019 cibiyar bincike da wayar da kan al’umma akan yanar gizo ta Sharfadi.com hadin gwiwa da wasu kungiyar International Center for Leadership and Enterpreneurship (ICLEAD) da Kano Youth Colation for Advocacy and Development (KAYCAD) suka gabatar da taro na musamman domin tattauna batutuwan da suka shafi gudummuwar da ‘yan social media zasu bayar a ranar zabe.

Taron ya sau halartar jami’an hukumomi daban-daban, kungiyoyi da kamfanunuwa da jami’an kafafan yada labarai da kuma tarin ‘yan social media da dama.

An gabatar da jawabai kala-kala a wurin taron.

Baban sakon da aka aike dashi a taron shine masu amfani da shafukan sada zumunta su kauracewa yada sakamakon karaya ko labaran tarzoma a ranar zabe.

Allah ya taimaka ya sanya ayi zabe lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.