JAHOHIN DA ABU ZARIA SUKA FI BASU ADMISSION

A kakar karatu ta shekarar 2017/2018 Ahmadu Bello University, Zaria ta dauki dalibai Dubu goma da dari daya da Arba’in (10, 140).
A cikin wannan adadin ga daliban Jihohi hudu da ABU din tafi bawa gurbin karatu (admission)

1. Kaduna State
An dauki dalibai yan Asalin Jihar Kaduna su dubu biyu da dari hudu da tamanin da daya (2,481)

(Yayin da ita kuma BUK ta dauki dalibai Yan Asalin Jihar Kano su dubu hudu da dari biyar da hamsin da uku, 4,553, Kalubalen ku masu Cewa BUK bata cika bawa Yan Kano Admission ba)

2. Kogi State
Hakanan an dauki dalibai yan asalin Jihar Kogi su dari takwas da tis’in da takwas (898)

3. Kano State
Inda su kuma kanawa suka rabauta da gurbin karatu na dalibai dari takwas da Saba’in da hudu (874)

4. Katsina State
Yayin da Katsinawan Dikko suka kwashe gurbin karatun daliban da yakai dari bakwai da Ashirin da takwas (728)

Leave a Reply

Your email address will not be published.