Adadin dalibanda suka samu admission na makarantar gaba da sakandari daga 2008 zuwa 2017

Ga adadin Daliban da suka samu gurbin karatu a makarantun gaba da Sakandare tun daga Shekara ta dubu biyu da takwas (2008) har izuwa ta dubu biyu da sha Bakwai (2017)

1. 2008
A Shekarar 2008
Dalibai dubu dari uku da sittin da daya da dari takwas da biyar ne suka samu shiga Makarantun gaba da Sakandare (361,805)

2. 2009
Inda a Shekarar 2009 adadin ya karu zuwa Dubu dari hudu da tara da dari takwas da tamanin da takwas (409,888)

3. 2010
Haka kuma a Shekarar 2010 dalibai dubu dari hudu da saba’in da tara da dari biyar da talatin da tara ne suka shiga makarantun gaba da Sakandare (479,539)

4. 2011
Sai dai kuma a Shekarar 2011 adadin daliban ya ragu, inda aka samu daliban da suka shiga makarantun gaba da Sakandare su dubu dari hudu da Sittin da takwas, da dari hudu da Arba’in da takwas (468,448)

5. 2012
Saidai a Shekarar 2012 adadin yayi tashin gwauron zabi inda yakai Dubu dari hudu da tis’in da bakwai da dari hudu da Ashirin da bakwai (497,427)

6. 2013
To amma kuma sai shekarar 2013 tace bani guri, inda aka samu dalibai Dubu dari Biyar da goma sha uku da dari biyu da bakwai da suka shiga makarantun gaba da Sakandare (513,207)

7. 2014
A Shekarar 2014 kuma sai adadin ya ragu sosai inda aka samu dalibai Dubu dari hudu da sittin da bakwai da saba’in da hudu da suka shiga makarantun gaba da Sakandare (467,074)

8. 2015
A Shekarar 2015 kuma sai farashin ya daga inda aka samu dalibai Dubu dari biyar da Ashirin da biyu da dari takwas da hamsin da shida da suka shiga Makarantar gaba da Sakandare (522,856)

9. 2016
Kana dai likafa ta cigaba a Shekarar 2016 inda aka samu dalibai Dubu dari biyar da sittin, da dari tara da ashirin da biyar da suka shiga Makarantar gaba da Sakandare (560,925)

10. 2017
Hakama Shekarar 2017 itama dalibai Dubu dari biyar da sittin da shida da dari shida da Arba’in da daya ne suka shiga Makarantar gaba da Sakandare (566,641)

11. 2018
A Yayin da ita kuma Shekarar 2018 ba’a fitar da nata ba, sakamakon wasu makarantun na gaba da Sakandare har Yanzu basu gama admission din nasu ba

Leave a Reply

Your email address will not be published.