TASBIHI A BAYAN SALLAR FARILLAH KALA SHIDA NE

TASBIHI A BAYAN SALLAR FARILLAH KALA SHIDA NE

Ibn Usaimeen Allah yayi masa Rahama yana cewa:
*”Ga dukkan wanda yake so yabi sunnar Manzon Allah SAW kuma ya dace da ita yana da qa’idodi guda uku”*

1-Qa’ida ta farko
*”Kayi kokarin aiki da wannan sunnar da kokarin kiyayeta batare da kariba ko ragi”*

2-Qa’ida ta biyu
*”Kiyaye sunnar kamar yadda tazo kada a mantata ko a ki aiki da ita”*

3-Qa’ida ta ukku
*”Aikata sunnar a matsayin koyi da Manzon Allah SAW ba al’adaba ko kaga mutane sunayin hakan,kaji kanayin koyine da Annabi s.a.w”*

*_1-SIGA TA FARKO_*
-Subhãnallah 33
-Walhamdulillah 33
-Wallahu Akbar 33
Sai a cike na dari da
-ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ . ﻟﻪ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻗﺪﻳﺮ .
_Lã ilaha illallahu wahdahu lã sharika lahu lahul mulku walahul Hamdu wahuwa ala kulli shai’in Qadir_
Manzon AllaH SAW yace:
*(Wanda ya fadi wannan bayan kowace sallar farilla, an gafarta masa zunubansa ko da sun kai yawan kumfar teku)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ

*_2-SIGA TA BIYU_*
-Subhãnallah 33
-Walhamdulillah 33
-Wallahu Akbar 34
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Wanzazzune mai fadarsu ko mai aikata su baya tabewa,Subhãnallah 33,Walhamdulillah 33,Wallahu Akbar 34 a bayan kowace sallar farilla)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ

*_3-SIGA TA UKKU_*
-Subhãnallah 10
-Walhamdulillah 10
-Wallahu Akbar 10.
Sukace ya Manzon Allah,ma’abuta dukiya sun tafi da daraja madaukakiya da ni’ima tabbatacciya,sai yace:
*(Ta yaya hakan??)*
Sai sukace;
“Suna yin sallah kamar yanda muke yin sallah,suna jihadi kamar yanda muke jihadi,sannan suna ciyarwa da sauran dukiyarsu,mu kuma bamu da dukiya. Sai Manzon Allah s.a.w yace:
*(Shin bazan baku labarin wani abu ba?? Wanda zaku kamo wanda ya wuceku,kuma ku tserewa wanda yake bayanku,kuma babu wanda zaizo da irin abinda kuka samu sai wanda ya aikata irin abinda kuka aikata,kuyi*; Subhãnallah 10
-Walhamdulillah 10
-Wallahu Akbar 10, a bayan kowace sallah ta farillah)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ

*_4-SIGA TA HUDU_*
-Subhãnallah 25
-Walhamdulillah 25
-Wallahu Akbar 25.
@ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ.

*_5-SIGA TA BIYAR_*
-Subhãnallah 33
-Walhamdulillah 33
-Wallahu Akbar 33
Talakkawan Madina sunzo wajan Manzon Allah SAW,sai Sukace ya Manzon Allah,ma’abuta dukiya sun tafi da daraja madaukakiya da ni’ima tabbatacciya,sai yace:
*(Ta yaya hakan??)*
Sai sukace;
“Suna yin sallah kamar yanda muke yin sallah,suna yin azumi kamar yanda muke yin azumi jihadi kamar yanda muke jihadi,sannan suna ciyarwa da sauran dukiyarsu,mu kuma bamu da dukiya. Sai Manzon Allah s.a.w yace:
*(Shin bazan baku labarin wani abu ba?? Wanda zaku kamo wanda ya wuceku,kuma ku tserewa wanda yake bayanku,kuma babu wanda zaizo da irin abinda kuka samu sai wanda ya aikata irin abinda kuka aikata,kuyi; -Subhãnallah 33
-Walhamdulillah 33
-Wallahu Akbar 33 bayan kowace sallar farillah)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ.

*_6-SIGA TA SHIDA_*
-Subhãnallah 11
-Walhamdulillah 11
-Wallahu Akbar 11
@ﺃﺧﺮﺟﺔ ﻣﺴﻠﻢ.

Wadan nan sune sigogin Tasbihin da ya tabbata a sunnar Manzon Allah SAW ya kamata ga dukkan musulami ya riqa yin wadan nan Tasbihi yana chanchanzawa lokaci zuwa lokaci dan ya yi aiki da koyi da Manzon Allah gaba daya.

   *_Allah ne mafi sani_*

Leave a Reply

Your email address will not be published.