GA WASU GIDAJE GUDA 3 A ALJANNAH KO WANI ZAI YI RABON SAMUN KO DA DAYA NE

*GA WASU GIDAJE GUDA 3 A ALJANNAH KO WANI ZAI YI RABON SAMUN KO DA DAYA NE* 👉🏾
.
Manzon Allah (s.a.w) yace:

1. “Na lamunce gida a farkon Aljannah ga duk wanda ya bar *musu* ko da yanada gaskiya.
.
2. “Na lamunce gida a tsakiyan Aljannah ga duk wanda ya bar *karya* ko da wasa ya ke.
.
3. Na lamunce gida a madaukakiyar Aljannah ga duk wanda ya *kyautata* dabi’unsa”.
.
📚 Abi Dawud, Hadisi na 4800, Sahihul Jami’i, Hadisi na 1464
.
Mafi yawancin musun da mukeyi bai da amfani garemu, kuma ya kan kare da bacin rai.
Musun Siyasa ya yi mana yawa. Kuma ma fi yawanci ma muna fadin abinda muka ji ne, ba abinda muke da shaida ba.
.
Karyar wasa kam ba’a magana. Kamar kace wani Bafulatani ya yi kaza da kaza, musamman don a yi dariya, ko wata karya ta wasa.
Kyautata dabi’u an masa fassara da dama. Daga cikin husnul khulq akwai; hakuri, kunya da tawakkali. A wata fassarar kuwa; sakin fiska, yada alkhairi. A wata fassarar kuwa; yafiya, umarni da alkhairi da kauda kai ga barin jahilai.
.
Allah Ka Sa Mu Dace Ka Sanyamu Cikin Wadanda Za Ka Yiwa Gam-Da-Katar Ka Shigar Da Mu Aljannah Da FalalarKa.
Ya Allah Ka Bamu Shugabanni Wadanda Suke Su Ne Mafi Alkhairi Garemu, Kar Ka Dubi Wadanda Muke So Ko Wadanda Ba Ma So, Ya Allah Ka Dubi Wadanda Su Ne Alkhairi A Garemu Ka Basu Nasara A Dukkan Zabukan Da Za’a Yi Gobe.
.
Ina Mana Fatan Alkhairi A Zabukan Gobe Asabar.
.
Abu Albani
15/February/2019

Leave a Reply

Your email address will not be published.