SIYASAR DIMOKARADIYYA RIKITACCEN AL’AMARI.

SIYASAR DIMOKARADIYYA RIKITACCEN AL’AMARI.

MUGUN WASA, SHU’MIN GASA.

Siyasar dimokaradiyya wani rikitaccen  al’amari ne, mai wuyar fahimta, an tabbatar da cewa, dimokaradiyya wasan yawan jama’a ne, wanda ya sami fifikon yawan jama’a ya sami nasara, wadanda su ka fi kowa yawa su ke da rinjaye, ‘yanci ne ga talaka, ga kuma ‘yancin fadin albarkacin baki, kuma kalmar ‘Democracy’ ta na nufin karfi da iko ya koma ga hannun talaka, wannan a rubuce ke nan, kuma haka mutane su ke kallon wannan tsari na mulkin dimokaradiyya.

Dauloli da kasashe a baya, sun yi amfani da tsarin zaban shugaba jagora ta hanyar kada quri’a, wanda ya sami quri’a ma fi rinjaye ya zamo shugaba, dauloli da dama sun gudanar da wannan tsari, inda a ka rika amfani da hanyar kada quri’a wajen zaban shugaba, ta hanyoyi guda biyu, hanyar shura wato kididdigaggun mutane kadan su yi quri’a a tsakaninsu, ko kuma hanyar amfani da gama garin jama’a wato fitowar dukkannin jama’a domin zabar dan takara.

An soma kada quri’a domin zabar shugaba a daular Rumawa ne a tsakiyar qarni na biyar kafin zuwan Annabi Isah A.S. wato 507B.C. a birnin Athens, inda su ka rika yin zaɓe da wani salon siyasar dimokuraɗiyya mai suna ‘Athenian Democracy’. Daga nan dauloli da dama sun rika bijirewa tsarin mulukiyya su na komawa kan tsarin dimokuraɗiyya wanda ya ke bai wa kowa ‘yancin tsunduma cikin harkokin mulki domin a dama da su.

A tarihin Musulunci, an soma zaben shugaba ne ta hanyar dimokaradiyya a zamanin Khalifa Usman bn Affan a zamanin mulkin Rashidun, inda majalisar shura ta zabe shi, sai dai daga baya Khalipha Mu’awiya bn Abu Sufyan ya dakile wannan ‘yancin, inda ya mayar da Khaliphancin bisa tsarin Mulukiyya, kuma wannan shi ne tasgaron da tsarin dimokuraɗiyya ta yi ta cin karau da shi tun farko har zuwa karshen zamanin ‘Midieval ages’ 10-17 century A.D. matsalar ita ce, duk yadda a ka shimfida wannan tsari na dimokuraɗiyya daga karshe rikici ne ke barkewa tsakanin bangarorin da ke da ruwa da tsaki a harkokin mulkin, inda bayan sun yi dauki ba dadi, an zubar da jini mai yawa, bangaren da ta fi karfi ta ci nasara sai ta kwace mulkin, daga karshe idan ta dare bisa gadon mulkin sai ta maida shi na gadon gado.

A wannan zamanin da mu ke ciki, Turawan yamma, bayan sun kame kasashen duniya ta hanyar yi masu mulkin mallaka, sun sake dawowa da wannan dadadden tsarin na dimokuraɗiyya amma sun sake mashi fasali da salo, yadda daga kasashensu za su rika ɗorawa da sauke shugabannin kasashen duniya lokaci bayan lokaci, ta hanyar da babu wani rukuni na mutane da zai rika yi masu katsalandan, balle har wani bangare na mutanen wata kasa su kwace karfin iko da mulki. Turawan Yamma sun yi amfani da dibarar canja salon tsarin dimokuraɗiyya daga yadda a ka santa tun asali, idan ku na tunkaho da yawan jama’a ne, sun canza tsarin zuwa wani salo, salon da ya kakkabe karfin da masu rinjaye su ke da shi a kasa, ya karfafi marasa rinjaye ‘yan tsiraru kuma ya ba su kariya, a wannan sabon tsari na dimokuraɗiyya, a zahirance an sanya cin nasara ne ga wanda ya  sami quri’u mafi rinjaye daga wurin talakawan da za a mulka, amma ta karkashin kasa ba haka abin ya ke ba, ashe sun yi wa abin wani tsari ta karkashin kasa, ba quri’ar talaka kawai ke da tasiri ba, rukunan mutane guda uku ke da tasirin gaske a siyasar dimokuraɗiyya ta wannan zamani, rukunin farko ‘International Communities’ (kasashen Yamma masu ƙarfin faɗa a ji a duniya) rukuni na biyu ‘Secrete government’ ko kuma ‘elite’ wato rukunin mutane masu ƙarfin faɗa a ji a cikin kasa, masu rike da akalar tattalin arzikin kasa, wadanda su ka shake makogoron masu rike da madafun iko, sai rukuni na uku gama garin talakawa masu jefa quri’a.

Wani yawo da hankalin talaka da su ka yi shi ne, sai a ka rubuta cewa, quri’ar talaka kawai a ke bukata domin gudanar da wannan zaɓe, har a ke rera kirarin cewa, quri’arka ‘yancinka! Ina ashe a ta karkarshin ƙasa ba haka abin ya ke ba, a na bukatar abubuwa ne har rukuni uku, (a) jami’an tsaro da karfin soji, (b) kudi da ƙarfin tattalin arziki, (c) katin zabe wato quri’a.

(a) Mallakan jami’an tsaro da ƙarfin soji, a tsari irin na zamanin nan a zahiri ya ta’allaka ne a wuyan gwamnatin kasa, amma a ta karkashin kasa a na jujjuya akalar tsaron duniya ne daga cibiyar tsaron kasashen Yamma, tare da ba da umarni.

(b) Harkokin kudi da abin da ya shafi tattalin arziki, jam’iyyun siyasa su ma kasashen Yamma ke juya shi, ta hannun ‘elite’ wato mala’u ko kuma abin da a ka fi sani da ‘secrete government’ masu ƙarfin faɗa aji tare da jan ragamar tattalin arzikin kasa.

(c) Katin zabe shi kuma a hannun talaka ya ke, mallakarsa ce, shi ke da ikon sarrafa ta, wajen yin amfani da ita domin zaben wanda ya ke ganin shi ne maslahar rayuwarsa, sai dai kuma, babu yadda zai iya kaucewa tasirin ƙarfin soji, da ƙarfin tasirin kudade a ranar zabe har sai ya kasance dukkan illahirin talakawan kasar kansu a hade ya ke, su kan iya yin magana da murya daya, domin aiwatar da abin da ya shafe su. A dai dai wannan gabar, wadancan rukunonin farko da na biyu, kasashen Yamma da kuma masu ƙarfin faɗa a ji a cikin kasa sun riga sun shafe ƙarfin talaka da ƙarfin katin zaben da ke hannun shi talakan, ta dalilai kamar haka:-

i. Rukunin kasashen Yamma da na masu ƙarfin faɗa a ji su su ke tafiyar da harkokin tsaron kasa, babu hannun talaka a ciki.

ii. Rukunin kasashen Yamma da masu ƙarfin faɗa a ji su su ke da mallakar tattalin arziki mai karfin gaske, da kuma harkokin jam’iyyun siyasa, talaka kuwa sai hange.

iii. Rukunin talakawa kuwa an riga an shafe ƙarfin da su ke da shi, ta hanyar kakkasa su gida gida, yanki yanki, qabila qabila, banbancin addini, Kudu da Arewa, kai kowane rukuni na talakawa an keta su gida biyu ko kuma fiye da haka, Musulunci (Izala 1&2, darikar Qadiriyya da Tijjaniyya, Salafiyya mabiyan malamai kashi kashi, Shi’ah Zazzakiyya da ‘yan RAAF). Addinin Kirista kuwa su ma an karkawar su zuwa (Orthodox, Catholic, mabiya cocin ‘yan Protestants Kashi kashi iya ganinka), duk bangaren da ya tubure a gefensa, sai a dauko daya bangaren su yi amfani da shi, wannan shi ya sa quri’ar talaka ba ta da wani tasiri a tsarin dimokuraɗiyya, domin duk abin da a ka keta shi gida gida karfinsa ya tafi, ba shi da tasiri kwatanta kwata.

Abin da ya ragewa talaka a siyasar dimokuraɗiyya shi ne ciniki, nawa za a ba shi, wato masu ƙarfin tattalin arziki da na soji su saye shi ta hanyar rarraba masu abubuwan da za su jawo hankalin talaka.

Wannan shi ne shu’umcin siyasar dimokuraɗiyya da mu ke fama da shi a wannan zamanin, wato yadda International Communities da elites na kasashen duniya su ke yawo da hankalin talaka da sunan siyasar dimokuraɗiyya, alhalin duk cikin tsarin babu inda talaka ya ke da ta cewa, balle kuma har yin ittifakinsa a kan wani dan takara ya yi tasiri, abin da talaka ya kamata ya yi shi ne, ya mike tsaye ya zabi wakilan majalisun jihohi gwamna da wakilan majalisar tarayya wadanda za su amfane shi, domin su ne quri’arsa zai iya yin tasiri wajen zabensu, amma gwamnatin tsakiya quri’ar talaka ba ta da tasiri a kanta.

Misali zabukan 1999, 2003, 2007, 2011, an yi shi ne tsakanin bangaren International Communities+Elites+Ruling Class da kuma dandazon talakawa a gefe guda, talaka ya na ji, ya na kuma gani a ka gwabje shi.

Zaben 2015 kuwa ya gudana ne tsakanin International Communities+Elites+dandazon talakawa da kuma Ruling Class a gefe guda, inda a ka gwabje bangaren Ruling Class.

Wannan karon kuwa, za a fafata ne tsakanin International Communities+Elites da kuma bangarorin Ruling Class+dandazon talakawa a gefe guda, Allah kadai ya san wandanda za su ci nasara.

Babu abin da ya fi zamowa alkhairiy ga talaka kamar ya boye zabinsa a cikin ransa,   shugabannin  addinai su bar kowa ya zabi cancanta, talakawa su shiga cikin kowace jam’iyya a fafata cikin lumana, Malamai su tsaya a magada Annabawansu, ‘yan siyasa su yi siyasa mai tsabta, ranar zabe kuma kowa ya bayyana ra’ayinsa a akwatin zaben unguwarsu. Idan ba haka ba kuwa, za a ci gaba da ta da jijiyoyin wuya, a lokacin da rukunin bangarorin kasashen Yamma da na masu fada a ji cikin kasa, su ke shirya yadda za su ci gaba da makure wuyan rukunin talakawa.

Dimokuraɗiyya ke nan shu’min al’amari.

Allah ya kai mu gobe Asabar 16/02/2019. Domin zabar wadanda za su shugabanci al’amarin musulmi ameen.Yyy

Leave a Reply

Your email address will not be published.