[[INEC Baku kyauta ba]] Kun tura ma’aikatan ku na Adhoc staff zuwa kauyuka, yaya kukeso suyi yanzu??

Maganar #Gaskiya

Akoi bukatan Hukumar Zabe mai Zaman kanta na kasa da tayi dubi, izuwa ga al-ummah da ta dauka wato (Ad-hoc Staff) nata domin su taimaka mata yayin gudanar da aikin na zabe na 2019. Wanda ahalin yanzu an dage wannan zaben sannan kuma mutanen nan sunje su, wuraren aikin su na na wuchen gadi. kamar yadda hukumar zaben ta umarce su.
     A tawa Fahimtar wayen nan bayin Allah dukkan su baki daya sun chan-chanci karban kudin aikin su (allowance). don hada akoi bukatar hukamar zabe tayi nazari akan wayen nan bayin Allah.

Abun Lura
1. Wayen nan copers da ma wayen da ba copers ba (Ad-hoc din baki daya) sunci fiye da rabin lokacin aikin da zasuyi na zabe. kasancewar sabon salo na kwana a gurin da zakayi aiki.

2. Tabbas zuciyarsu a ciki yake da soyayyar kasan nan. dalili itace. Duk inda aka turasu babu wayen da akabawa kudin loji ko kuma kudin tuwo, kai harma takai zakaga wasu a street suka kwana kuma aka wayi gari wai an daga zaben.

3. tabbas biyan su kudin aikin su zai kara musu karfin guiwa wajen kuma dawowa domin yin aikin tare da bin dokokin aikin kamar yadda yake, domin suma zasu san anyi dasu kuma ana tare dasu. sannan suna da muhimmanci sosai a cikin tafiyan.

Daga karshe yin hakan zai kara daukaka hukumar zaben da ma kasar baki daya. sannan hakan a fahimtata itace adalci ga ma aikata na wuchen gadi na zabe. Ubangiji Allah shi tabbatar mana da alkhairin sa, ya kuma zaba mana shugabanni na gari masu kaunar mu bawayen da muke son subah. Allah muka kara rokon ka, da kasayi wannan zaben lafiya agamata lafiya sati mai zuwa a dukkanin fadin kasar nan. Ameeeen

#KBD Logistics
16th February 2019

Leave a Reply

Your email address will not be published.