Shugaban IZALA na Jahar Bauchi ya Karrama Darakta “Jibwis Social Media”

Shugaban IZALA ya Karrama Darakta “Jibwis Social Media”

A maraicen Larabar nan Shugaban IZALA na jihar Bauchi Alhaji Muhammad Inuwa ‘Dan Asabe ya karrama Darakta ‘Jibwis Social Media’ na kasa, Alhaji Ibrahim Baba Suleiman bayan ya kammala gabatar da takarda akan “ILLAR BANGAR SIYASA A KAFAR SADARWA”.

An gudanar da taron ne a wajen taron karawa juna sani da kungiyar IZALA ta Bauchi Zone ta shirya, kuma ta gabatar, karkashin jagorancin Shugaban JIBWIS ta Bauchi Zone Alhaji Sadisu Alhaji Sani.

A cewarsa Shugaba Inuwa Dan Asabe, yace “Mun karrama Ibrahim Baba ne saboda kokarin sa wajen gudanar da aikin da aka saka shi, da kuma irin yadda yake tafiyar da aiki ba tare da gajiyawa ba, kazalika munga ya tsaftace harkar ‘Jibwis Social Media’ wadanda suke karkashin ikonsa” andaina zage zage ga Malamai masu da’awa dan banbancin Ra’ayi, sannan ya taka burki ga mambobin kwamitin wajen rubuce rubuce Wanda babu gaira babu dalili. Bisa wannan dalili ne muka gayyato shi jihar Bauchi, Muka karrama shi, domin mu kara masa karfin Gwuiwa.” Inji Shi.

Tun farko a bayanan sa, shugaban JIBWIS na Bauchi Zone, Alhaji Sadisu Alhaji Sani, yace munyi wannan karramawa ne domin karfafa gwuiwa ga Darakta Ibrahim Baba, saboda gamsuwar mu Da yadda yake kokarin kawo ayyukan ci gaba a harkar ‘Social Media na kungiyar IZALA a fadin kasar nan da kasashen ketare.

A karshe Ibrahim Baba Suleiman, yayi jawabin godiya, tare da fatan Allah ya amshi ayyukan da muke gabatarwa kullum, ya kuma yabawa shugaban IZALA Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau da yan majlisar sa, Wanda shi ya assasa wannan kwamiti ya kuma yi tsayuwar mai daka, domin ganin kwamitin ya tsayu da kafafuwar sa.

Dukkan wakilai na kungiyar IZALA na kasa, jiha, da kananan hukumomin dake karkashin Bauchi Zone duk sun samu halarta.

Kazalika Shugaban ‘JIBWIS Social Media, Muhammad Nasir da yan majalisar sa, da shugaban Jibwis Social Media na Bauchi Zone, Abdulmalik Abubakar Aliyu da yan majalisar sa, duk sun samu hakarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.