ILLOLI GUDA SHIDA-6 GA MASU YANKE ZUMUNCI

ILLOLI GUDA SHIDA-6 GA MASU YANKE ZUMUNCI:

Mai ake nufi da yanke zuminci??
*Shine mutum ya yake alqar dake tsakaninsa da yan uwansa ko danginsa,baya zuwa gaidasu ko baya taimakonsu ko baya yin mu amala dasu,ya dai yanke duk wata alaqar da Allah ya sanya a tsakaninsu.yake zuminci yana cikin manyan zunubai wadanda Allah baya yafewa sai ta hanyar Tuba ingantacce*.

Ga kadan Daga Cikin Illolin Yanke zuminci.

*1-Allah baya karbar aiyukan mai yake zuminci*.

Annabi s.a.w yana cewa:
*”Ana bujuro da aiyukan baya zuwa ga Allah akowace ranar alhamis daren juma’a(wato alhamis da dare),amma ba’a amsar aiki mai yake zuminci”*
@Albany yace Hadisine Hasan. Saheehut Targheeb-2538
Ahmad-2/484

*2-Allah yana Gaggauta yi masa azaba tun daga nan Duniya*

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
“Babu wani laifi da Allah yake gaggauwar yin Uquba ga minyinsa anan duniya tare da yimasa tanadin wani azabar alahira kamar;Mugunta da Yanke zuminci”.
@Ahmad da Abu Dauda.
Albany yace Hadisine Saheehi(Assahee
ha-2/907)

*3-Mai yanke zuminta yana ganin sakamakon Abinda ya aikata anan duniya kafin mutuwarsa(Abinda hausawa suke cewa zai girbi abinda ya shuka)*.

Annabi s.a.w yana cewa:
(Duk wanda ya yake zuminci,ko ya rantse da wata rantsuwa ta karya,zai ga sakamakonsa kafin ya rasu).
@Baihaqee Albany ya ingantashi. (Assaheeha-1121.)

*4-Yanke zuminci yana janyowa mutum La’antal Allah da azabarsa*

Allah yana cewa:
(ﻓَﻬَﻞْ ﻋَﺴَﻴْﺘُﻢْ ﺇِﻥْ ﺗَﻮَﻟَّﻴْﺘُﻢْ ﺃَﻥْ ﺗُﻔْﺴِﺪُﻭﺍ ﻓِﻲ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ﻭَﺗُﻘَﻄِّﻌُﻮﺍ ﺃَﺭْﺣَﺎﻣَﻜُﻢْ) ‏( ﺃُﻭﻟَٰﺌِﻚَ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻟَﻌَﻨَﻬُﻢُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻓَﺄَﺻَﻤَّﻬُﻢْ ﻭَﺃَﻋْﻤَﻰٰ ﺃَﺑْﺼَﺎﺭَﻫُﻢْ)
@Surat Muhammad 22-23]

Kuma Allah yana cewa:
(ﻭَﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳَﻨْﻘُﻀُﻮﻥَ ﻋَﻬْﺪَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻣِﻦْ ﺑَﻌْﺪِ ﻣِﻴﺜَﺎﻗِﻪِ ﻭَﻳَﻘْﻄَﻌُﻮﻥَ ﻣَﺎ ﺃَﻣَﺮَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺑِﻪِ ﺃَﻥْ ﻳُﻮﺻَﻞَ ﻭَﻳُﻔْﺴِﺪُﻭﻥَ ﻓِﻲ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ۙ ﺃُﻭﻟَٰﺌِﻚَ ﻟَﻬُﻢُ ﺍﻟﻠَّﻌْﻨَﺔُ ﻭَﻟَﻬُﻢْ ﺳُﻮﺀُ ﺍﻟﺪَّﺍﺭِ)
@Surat Ar-Ra’d 25]

*5-Mai yake zuminci Allah baya sadar shi ga rahamasa*.
@Bukhari

*6-Yanke zuminci aikine da yake janyo fishi Allah ga mai yinsa*.
@Assaheeha-2522.

*Allah ka bamu ikon sadar da zumincin da yake kanmu,ka kuma karemu daga yanke zumunta*.

1 thought on “ILLOLI GUDA SHIDA-6 GA MASU YANKE ZUMUNCI

Leave a Reply

Your email address will not be published.