YA KAMATA AKAN KOWANE MUSULMI YASAN WADAN NAN KALMOMI

*_YA KAMATA AKAN KOWANE MUSULMI YASAN WADAN NAN KALMOMI_*

Mafi shiriya itace shiriyar Annabi SAW kuma mafi koyarwa itace koyowar Annbabi SAW,babu wata damuwa da zata sami musulmi face ya sami waraka daga wannan damuwar da izinin Allah abisa koyarwar Annabi SAW.

Annabi SAW ya koyar da Sahabban sa hanyar samun waraka daga dukkan kunci da damawar rayuwar duniya.

Daga Ibn Mas’ud R.A yana cewa:
“Lallai Manzon Allah SAW yace:
*(Babu wani bakin ciki ko damuwa da zai samu bawa duk girmanta ko kankantarta,sai yace*:
_”اللهم إني عبدك ، وابن عبدك ، وابن أمتك ، ناصيتي بيدك ، ماض في حكمك ، عدل في قضاؤك ، أسألك بكل اسم هو لك ، سميت به نفسك ، أو أنزلته في كتابك ، أو علمته أحدا من خلقك ، أو استأثرت به في علم الغيب عندك ؛ أن تجعل القرآن ربيع قلبي ، ونور صدري ، وجلاء حزني ، وذهاب همي”_.
*Face sai Allah ya tafiyar masa da wannan bakin cikin da damuwar kuma ya maye masa gurbinsa da farin ciki da jin dadi)*.
Sai Ibn Mas’ud R.A yace:
“Ya manzon Allah ya kamata mu san wannan kalmomi kuma mu kiyaye su” sai yace:
“(Ka kyauta hakane wanda yaji wadan nan kalmomi su koyar da su)*.
@صحيح الترغيب والترهيب (1822).

Allah ka yaye mana dukkan bakin ciki da damuwar duniya da lahira.

_”اللهم إني عبدك ، وابن عبدك ، وابن أمتك ، ناصيتي بيدك ، ماض في حكمك ، عدل في قضاؤك ، أسألك بكل اسم هو لك ، سميت به نفسك ، أو أنزلته في كتابك ، أو علمته أحدا من خلقك ، أو استأثرت به في علم الغيب عندك ؛ أن تجعل القرآن ربيع قلبي ، ونور صدري ، وجلاء حزني ، وذهاب همي”_

Leave a Reply

Your email address will not be published.