Hakikanin Abinda Ya Faru Yau a Hukumar Hisbah game da rufe ofishin Daurawa a Kano

[Siyasar Kano] Hakikanin Abinda Ya Faru Yau a Hukumar Hisbah

Acikin makon da ya gabata ne babban kwamandan hukumar hisbah ta jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya jagoranci tawagar alarammomi guda 100 da malamai na bangarori daban-daban zuwa gidan tsohon gwamnan jihar Kano Engr. Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso don nuna masa goyon baya akan kudurorinsa da dan takarar gwamna a jam’iyyar adawa ta PDP.

Ziyarar tazo ne kwanaki kadan da barkewar cece kuce kan zargin da wani tsagi na malaman kungiyar Izala sukayi na cewa Kwankwason yayi izgilanci a garesu.

Ziyarar su Sheikh Daurawa ta haifar da sabon cece kuce sosai a Kano, kwatsam kuma a yau sai muka samu sabon labarin barkewar dambarwa a hukumar Hisbah da Sheikh Daurawan ke jagoranta.

Wata majiya mai tushe daga hukumar Hisbah da ta nemi a sakaye sunanta ta bayyana min yadda al’amarin ya faru.

“Sheikh Daurawa bai koma office ba tun bayan waccan ziyarar da suka kaiwa Sanata Kwankwaso, sai dai a ranar asabar ya aika a sirrance an kwashe masa wasu daga cikin kayansa daga office din.

An bar office din a bude ana cigaba da gudanarwa inda sakatarensa ke lura da ofishin”.

A yau talata manyan jagororin hukumar sukayi meeting wanda akace an jima ba’ayi irinsa ba wanda ya hada manyan jami’an hukumar, bayan meeting din suka zartar da su rufe ofishin Sheikh Daurawan, sai dai koda suka nufi yin hakan sakataren Malam yayi tirjiya lamarin da yakai har anyi zage-zage a tsakani, a karshe dai mahukuntan hisban suka garkame ofishin babban kwamandan.

Majiyar ta tabbatar mana da cewa dama akwai jikakkiya tsakanin Kwamanda da kuma manyan jami’an hukumar wanda akan hakan ne ma aka dauki tsawon lokaci ba’a zaman meeting na jagororin hukumar.

Idan baku manta ba a kwanakin baya dai Sheikh Daurawa yayi Huduba akan zargin karbar nagoro da aka yiwa gwamna Ganduje wadda ta jawo masa  martani mai zafi ciki harda mai baiwa gwamna Ganduje shawara akan makarantun Allo Malam Albukhariy Mika’il inda ya shiga gidan Radio Rahama ya kalubalanci Sheikh Daurawa tare da zargin wasu badakaloli a hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa wato EFFC.

Allah Ya Kyauta.

Basheer Sharfadi
Young Journalist
19-02-2019.
#Hisbah #KNSG #PDP #APC #Kwankwaso #Ganduje

Leave a Reply

Your email address will not be published.