WAJIBINE GA DUKKAN MAI YIN SALLAH YA SANI

WAJIBINE GA DUKKAN MAI YIN SALLAH_*.

_Kyautata sallah da cika sallah da nutsuwa da tattara tunani waje guda lokacin yin sallah_

Daga Abi Hurairata رَضِيَ اللَّهُ عَنْه, Manzon Allah SAW yayi mana Sallah a wani yini, da ya gama sallar sai ya juyo yace:-
*(Yaa wane! Shin bazaka kyautata sallar ka ba?yanzu mai yin sallah ba zai Riqa dubiba yaya yake yin sallah, kuma yana yiwa kansa ne sallah,kuma Wallahi ni ina gani ta bayana acikin sallah, yaya kuke Ruku’u da Sujada, kamar yadda nake ganin ku a gabana)*
@صحيح مسلم – رقم : (423)

Daga Anas Ɗan Malik رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ, daga Annabi SAW yace:-
*(Ku daidaita acikin ruku’unku da sujadar ku ku kyautata su, domin wallahi ina ganin ku ta bayana, inda kunyi ruku’u ko kunyi sujada)*
@صحيح مسلم – رقم : (425)

Allah ka bamu ikon kyautatawa amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.