YAKAMATA SAURAN JAMI’OI SUYI KOYI DA JAMI’AR AHMADU BELLO DAKE ZARIA

YAKAMATA SAURAN JAMI’OI SUYI KOYI DA JAMI’AR AHMADU BELLO DAKE ZARIA*

By Ibrahim Assalafiy

 A duk Lokacin da aka tafi yajin Aikin Malaman jami’oi
Maaikatan jami’ar Ahmadu Bello Zaria,  Musamman shugabaninta sukan shiga damuwa kwarai, ganin cewa zaa birkita musu tsarin kalandar su ta wannan kakar karatun

Hakan yasa Shugabannin wannan makaranta basa wasa da kalandarsu

Hakan yasa bayan kungiyar Malaman jamioi (ASUU)Ta dage yajin aikinta, ABU tayi maza ta fitar da sabuwar kalandar ta ta zangon karatu a cikin kasa da kwana 6 da dage yajin aikin.

Wanda sauran shugabannin jamioin mu da dama har yanzu basu yi hakan ba a sauran makarantun mu

Hakan yasa muke jinjina ga ita wannan babbar jamia ta ABU Zaria·

kuma muke kira ga sauran jamioi da suyi koyi da ita.

KADAN DAGA CIKIN WASU BAYANAI DA YAKAMATA MU SANI DANGANE DA WANNAN JAMI’A TA ABU*

Ita dai wannan Jami’ar an kafata ne a 1962

A lokacin da aka fara karatu a cikinta tana affliated ne to Oxford University London, Ma’ana idan ka gama karatu a ABU a lokacin , ba Certificate din ABU za a baka ba, Certificate din Oxford university Zaa baka.

Tana daga cikin Manyan makarantun da ake daraja certificate dinka a ko ina a fadin duniya

An bata lambar girmamawa da ‘’Bigest University in sub-saharan counries‘’

Tana da kwararru kuma shahararrun malamai da masana da ake takama dasu a ko ina a duniya

Tana da cibiyoyin bincike masu yawa wanda gwamnatin tarayyah take matukar Amfana dasu

An cire manyan makarantu guda biyu a cikinta wadanda suma ake ji dasu a yanzu, daga cikin makarantu da aka Yaye su a cikin ABU harda:
ATBU Bauchi Da kuma BUK Kano.

Tana daya daga cikin jamioin sahun farko a nigeria kuma itace ta daya a arewacin kasar.

Tana da malamai kwararru dasu ke koyarwa a kasashen turai

Shi yasa muke fatan sauran Jami’in mu suyi koyi da ita , musamman ganin yadda take kokari da kazarkazar a wurin harkokin karatun ta

*#Rubutawa✍:*
Ibrahim Assalafiy(ASOF Chairman Kaduna State)

Leave a Reply

Your email address will not be published.