[[KA KARANTA]] TSARABAR YAU JUMA’A

TSARABAR YAU JUMA’A
              17-02-2017
.
1. Manzon Allah (s.a.w) yace: “Babu wani wanda zai yi wanka ranar Juma’a, ya yi kwalliya daidai gwargwado, ya shafa turare, sannan ya fita, bayan ya je Masallaci kuma bai keta tsakanin mutum 2 a sahu ba (ya zauna a inda ya samu waje ba sai da ya keta mutane domin isa gaba ba), sannan ya yi nafila na abinda ya sawwaka masa, sannan lokacin da Liman ke huduba ya yi shiru ya saurara, face sai an gafarta masa abinda ya yi na zunubi zuwa wata Juma’ar”.
Bukhari Hadisi na 843.
.
2. Manzon Allah (s.a.w) yace: “Duk wanda ya yi alwala, sannan ya kyautata alwalar, sannan ya je Juma’a, ya saurari Khuduba kuma ya yi shuru, za’a gafarta masa daga wannan Juma’ar zuwa wata Juma’a da karin wasu kwanaki uku, duk kuwa wanda ya yi wasa (da wani abu da zai dauke masa hankali lokacin Khuduba) to ya yi wargi (ya rasa ladan Juma’a).
Muslim Hadisi na 857.
.
3. Manzon Allah (s.a.w) yace: “Duk wanda ya karanta Suratul Kahfi ranar Juma’a, za’a haskashi da haske a tsakanin Juma’a guda biyu”.
Sahihul Jami’ Hadisi na 6407.
.
4. Manzon Allah (s.a.w) yace: “Ku yawaita Salati gareni ranar Juma’a da kuma daren Juma’a, duk wanda ya yi min Salati daya Allah zai masa Salati goma”.
Sahihul Jami’ Hadisi na 1209.
.
5. Manzon Allah (s.a.w) yace: “Ranar Juma’a akwai sa’o’i guda 12, babu wani da za’a sameshi a lokutan yana rokon Allah wani abu face Allah Ya bashi abinnan, ku nemi wannan lokacin a karshen sa’a bayan Sallar La’asar”.
Sahihun Nasa’i Hadisi 1389.
.
6. Shaikh Muhammad bn Saleh Al-uthaimin (rh) yace a ranar Juma’a akwai wasu sunnoni da akeson aikata su da suka hada da:
+ Karanta Suratul Kahfi
+ Wanka
+ Aswaki
+ Sanya Turare
+ Zuwa Masallaci da wuri
+ Sanya Tufafi mai kyau ko sabo ko tsoho
+ Yin addu’a domin samun dacewa da lokacin karbar addu’a
+ Yawaita Salati ga Manzon Allah (s.a.w)
Duba: Fataawa Muhimma Liyaumil Juma’a
.
7. Sallar Jumma’a wajiba ce, bai halasta barinta saboda wani dan karamin ciwo, ko makaranta ko makamancinsu.
Duba: Fatawar Lajnatud Da’imah 184/8
.
8. Sallar Juma’a ba ta halasta ga mutum a gidansa shi da iyalansa, idan kuwa sukayita to za su saketa a matsayin Azahar.
Duba: Fatawar Lajnatud Da’ima 196/8
.
9. Ba ya wajaba Sallar Juma’a a Masallaci ga Mata, su abinda ya wajaba musu shine su yi Sallar Azahar.
Duba: Fatawar Lajnatud Da’ima 196/8
.
10. Bai halatta ga wani yai magana a cikin Masallaci lokacin da Imam ke Khuduba.
Duba: Fatawar Lajnatud Da’ima 201/8
.
11. Ya halasta ga Liman yai magana da wani idan ta kama.
Duba: Fatawar Lajnatud Da’ima 202/8.
.
12. Idan mai Khuduba yai Salati wa Manzon Allah (s.a.w), ya halasta ga mai sauraro yai masa Salati ba tareda ya daga murya ba.
Duba: Fatawar Lajnatud Da’ima 217/8.
.
13. Duk wanda ya samu raka’a daya a sallar Juma’a, zai ciko raka’a daya kuma ya samu Juma’a.
Duba: Fatawar Lajnatud Da’ima 225/8
.
14. Mutum yai magana da wani ba Liman ba alhali Liman na Khuduba haramun ne.
Duba: Fatawar Lajnatud Da’ima 240/8
.
15. Bai halasta addu’a wa wanda yai atishawa, ko amsa sallama alhali Liman na Khuduba. Wannan shine mafi inganci cikin maganganun Malamai.
Duba: Fatawar Lajnatud Da’ima 242/8.
.
Daga:
 مجموعة خدمة إقرأ
Abu Albani
17-02-2017

Leave a Reply

Your email address will not be published.