Idan nasa ATM card a jikin ATM machine yana nunamin ATM blocked

Idan nasa ATM card a jikin ATM machine yana nunamin ATM blocked

Ga hanyoyi da zaka iya magance wannan matsala taka:
1. Idan ATM da kaje ba bankin ka bane, zaka iya kiran ma’aikatan wannan banki domin yi musu korafi, koko ka kira hotline dinsu.

2. Idan kana kusa da bankin ka, koko kana da damar zuwa bankin ka to kaje. Ka samu customer care wato mai kula da matsalolin jama’a na banki ka gaya mishi matsalarka cewa ya bude maka ATM dinka dake nuna blocked. Kada ka manta, kaje da ID CARD mai karfi kamar, katin dan kasa (National ID Card), shaidar tuki (Driving license) da sauransu. Banki suna buqatar wannan domin saukin aiki.

3. Zaka iya jira na awowi 24 (kwana daya kenan), kwana daya na cika zasu bude maka wannan blocked ATM dinka.

Zaka iya duba wannan shafin domin samun mafita ga wasu matsalolinka.

Zaka iya yi mana tsokaci (comment)  akan yadda muke gabatarda wannan shafi namu. Sai mun ji ku.

Abu Abdirrahman Kaltungo
CEO Arewagist.com.ng
[email protected]
23rd February, 2019.

Leave a Reply

Your email address will not be published.