Wanda yayita saka PIN a ATM har ATM yaki karban katinsa yaya zaiyi?

Wanda yayita saka PIN a ATM har ATM yaki karban katinsa  yaya zaiyi?

ATM machine yakan ki karban katin mutum ne, wato idan mutum yasa sai su dawo mishi dashi. Hakan yana faruwa ne sanadiyyar yayita shigar da numbobin sirrin shi ba daidai ba. A duk lokacinda hakan ya faru za suce maka ka jira kada kasa ATM dinka a kowa machine na tsawon awowi 24.

Galibin ATM machine yakan rike ATM na mutane ne idan suka saka numbobin sirri sau uku a take kuma ba daidai ba to ATM machine zai rike.

Saboda haka idan wannan matsala ta same ka, zakayi hakuri ne na awowi 24 ba tareda ka sake saka ATM dinka a kowanne machine ba, domin idan ka sake sawa a wani machine, machine  din zai iya rike maka ATM Card dinka, idan ya rike maka kuma sai ka bincika munyi rubutu kan yadda zakabi har ka samo abinka.

Idan kayi jira har na sawon awowi 24, bayan nan zaka iya zuwa ka cire kudinka a ATM machine ba tareda wata matsala.

Kada ku manta ku ajiye mana comment dinku a kasa. Mun gode.

Abu Abdirrahman Kaltungo
CEO Arewagist.com.ng
[email protected]
23rd February, 2019

Leave a Reply

Your email address will not be published.