[[JAMB 2019]] Ko Kasan zaka iya yin Upgrading (Converting) din Jamb dinka zuwa D.E

 ~Ko Kasan zaka iya yin Upgrading (Converting) din Jamb dinka zuwa D.E

Hukumar Shirya Jarabawar Share fagen shiga Jami’a ta Kasa (Jamb) a kakar karatu ta Shekarar 2019/2020  ta fitar da wani tsari mai ban sha’awa wanda a Shekarun baya babu irin shi.

Kamar Yadda kowa ya sani ana samun kuskure wajen Siyan E-pin na jamb, wanda zakuga madadin a siya maka na DE sai a kuskure a siya maka na jamb, to a wannan Shekarar Hukumar tayi kokarin ganin ta magance wannan matsalar ta hanyar bawa dalibai damar mayar da Jamb din su zuwa D.E  ba tare da wani chaji ba (na kudi)

Dan haka idan har ka samu irin wannan matsalar to ka kwantar da hankalin ka yanzu zaka iya canja ko mayar da Jamb din naka zuwa D.E

Haka ma misali: idan kayi Jamb kaga bakaci ba, to kuma kanada requirements na D.E  shima zaka iya canja jamb din zuwa D.E

Ko kuma idan ya kasance lokacin da ka siya Jamb dinka bakada requirements na D.E sai daga baya ka samu, shima zaka iya canja jamb din zuwa D.E.

Allah ya bada Sa’a

Leave a Reply

Your email address will not be published.