[[Abin tausayi]] Rayuwar wasu yan matan jami’a

WATA A JAMI’A Daga Abubakar Auyo
1) Ta samu gurbin ci gaba da karatu a wata jamia,  mahaifanta sun yarda da ita da tarbiyyar da suka ba ta sai suka amince ta tafi saboda abun da ta ke so kenan ci gaba da karatu. Saurayin da yake son ta shi ma ya ce ba komai zai jira ta.
2) Da ta  tsinci kan ta a bakon muhallin da  take ta muradin zuwa, ta hadu da sabbin mutane amma dai wadanda suka fi jan hankalinta sune irin wadanda ake kira da manyan yara, masu kai da gashi a cukurkude kamar shekar ungulu  da sa wanduna masu zama a rabin mazaunai kamar suna jin kashi, ga mota kuma duk wayoyinsu iPhone ne latest. Ita ma saboda kyan ta kuma saboda su mayun fararen mata ne ta ja hankalinsu
3) Lokaci ya tafi a yayin da alakarta da manyan yara ta fara nisa,  suna kashe mata kudi fiye da yadda ake ba ta a gidansu, a hankali sai ta yi watsi da wannan yardar ta mahaifanta, ta watsar da komai a yayin da yaudarar manyan yara ta rinjaye ta ta fara baza musu kafa.
4) Saurayinta na gida ya fara korafin ta daina daga wayarsa, abun da bai sani ba shine saboda yanzu tana rayuwa da manyan yara masu gashi ta fara ganinsa wani local, da wani sunansa Garba kamar garmar noma da kansa marar gashi kamar kabewa. Daga baya dai ya ga ba zai iya jura ba, ita ma kuma ta sanar masa ya hakura da ita ya nemi wata a makwabta daidai shi.
5) Lokaci yana ta tafiya har an yi shekara guda an dauki sabbin dalibai, shekar manyan yara ta fara tashi daga kan ta zuwa kan sabbin dauka,  ta neme su a waya da kuma a aji amma sun ki saurararta.
6) Da daddare ta kasa barci saboda tunane-tunane, ta janyo wayarta ta shigo facebook akalla ko za ta ga wani abu da zai debe mata kewa amma ba ta gani ba sai wanda yake shirin rusa mata kwakwalwa, saurayinta da ya ce zai jira ta ita kuma ta ce ya bar ta, ya bar ta din da dadewa kuma gashi yanzu ya dora katin daurin aurensa. Ta ji kamar duniyarta an dawo da ita sama na kallon kasa.
7) Ta kashe duk kudadadenta kuma in ta nema a gida sai ta yi awanni na bayanin abun da ta yi da su kafin ta samu wani, manyan yara sun koma da shekarsu kan wasu, abincinta ya kare. Tana ta tunanin neman mafita  kafin a karshe ta yanke shawarar ta kira tsohon saurayinta.
8) Ta kira shi ta ba shi hakuri, ya sanar mata komai ya wuce amma dai lokaci ya kure. Ta nemi ya taimaka ya ara mata kudi ko 3K ne, ya ce ba komai zai turo mata 5K kyauta, kuma bai kullace ta ba , za ma su iya zama abokai.
9) Ta yi kuka kamar ba gobe musamman ma lokacin da ta hau whatsApp ta duba status ta ga tsohon saurayinta ya dora hotonsa da wacce zai aura, ta ji kamar  ta tura masa da emoji na miciji saboda tsabar yadda ta ji ta tsane ta, amma dai ba ta yi ba.
 10) Bayan kwanaki da aladarta ta yi latti da kwana hudu da wasu bakin alamu, hankalinta ba karamin tashi ya yi ba, ta yanke shawarar ta yi pregnancy test. Ta siyo kit din, ta zo ta shirya komai ta tsaya tana kallon kit din a cikin tsananin damwua tana adduar kar layuka biyu su bayyana.
A karshe layuka biyun sun bayyana, ya bayyana tana da ciki. Ta yi nadama matsananciya, ta butulcewa yardar mahaifanta a kanta, ta bi son zuciyarta. Ta yi ihu, ta cukurkuda gashin kanta, ta daki gado kafin ta ji kamar ta kashe kanta.
Amma kuma kashe kai baya maganin damuwa ko ciwo, hasali ma dai damuwar ake rabawa dangi da masoya muddin rai!

Leave a Reply

Your email address will not be published.